



Hon. Salisu Muktari Ya Kaddamar da Tallafin Mai ga Boreholes/Famfuna Don Magance Karancin Ruwa a Potiskum
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
12 days ago
Shugaban Karamar Hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya kaddamar da rabon man dizil da fetur ga Boreholes/Famfuna a fadin karamar hukumar Potiskum, a wani yunkuri na rage matsalar karancin ruwa biyo bayan matsalolin wutar lantarki.
Shirin ya mayar da hankali ne kan famfunan da suka daina aiki sakamakon rashin wuta, musamman wadanda ke taka rawa gurin baiwa Samar wa al’umma ruwa a sassa daban-daban na karamar hukumar Potiskum din.
A karkashin wannan tsari, an bukaci masu fanfunan kasuwanci da su rage tare da daidaita farashin ruwa domin kaucewa jefa al’umma cikin wahala, haka kuma, an umarci famfunan gwamnati da na al’umma, da kuma wadanda kungiyoyi masu zaman kansu suka samar, da su yi aiki tukuru tare da cikakken karfi domin tabbatar da wadatar ruwa.
Da yake jawabi kan wannan shiri, Hon. Salisu Muktari ya yaba wa al’ummar Potiskum bisa irin goyon bayan da al'ummar karamar hukumar Potiskum suke baiwa gwamnatocin jiha da na karamar hukuma, yana mai cewa hakan ne ginshikin nasarorin da ake samu.
“Ina yaba wa al’ummar Potiskum bisa goyon bayan da suke ci gaba da baiwa gwamnati a kowane mataki, wannan hadin kai na taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da muke samu,” inji shi.
“Wannan tallafi ya shafi rijiyoyin gwamnati, wasu na ‘yan kasuwa da kuma na al’umma domin tabbatar da wadatar ruwa, ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan dama wajen kyautata hidima da kuma daidaita farashin Ruwan domin Al'umma su rayu cikin salama”
Ya kuma jaddada bukatar ganin duk wadanda suka amfana da tallafin sun sauke nauyin da ke kansu, ta hanyar samar da ruwa mai inganci da araha ga al’umma.
Ana kallon wannan mataki a matsayin wani gagarumin yunkuri na gwamnati wajen rage radadin karancin ruwa da kuma inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Potiskum.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa
Ofishin Shugaban Karamar Hukumar Potiskum.