



Ku Yi Wa Najeriya Addu’a, Ku Mara Wa Shugabanni Baya –Gwamna Buni Ga Malamai
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
6 days ago
—Sama da Malamai 800 Sun Hadu a Yobe Don Ƙarfafa Zaman Lafiya da Ci gaban Ƙasa
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ƙara dagewa wajen yi wa ƙasa addu’a, tare da yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni addu’ar samun nasara, yana mai jaddada cewa haɗin kai da zaman lafiya su ne ginshiƙan ci gaban ƙasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata muhimmiyar ganawa da sama da manyan limaman masallatan Juma’a 800 a fadin jihar, domin ƙarfafa rawar da malamai ke takawa wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai a al’umma.
Gwamna Buni ya bayyana cewa ƙasar na buƙatar taimakon Allah domin shawo kan ƙalubalen da take fuskanta, yana mai cewa akwai buƙatar haɗin kai da addu’o’i don tinkarar barazanar cikin gida da ta waje.
“Ƙasarmu na buƙatar addu’a domin samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba, dole ne mu mara wa shugabanninmu baya domin ciyar da Najeriya gaba,” in ji shi.
Yayin da yake tuna irin halin da aka shiga a lokacin Boko Haram insurgency, Gwamna Buni ya gargadi jama’a da kada su ɗauki zaman lafiyar da ake ciki yanzu da wasa.
Ya tuna irin asarar rayuka, rushewar dukiyoyi da kuma gudun hijirar da mutane suka fuskanta, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye zaman lafiyar da aka samu a halin yanzu.
“Ba za mu iya komawa irin waɗancan lokuta masu wahala ba, dole ne mu kare zaman lafiyar da muke da shi a yau,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa Najeriya na da muhimmiyar rawa a nahiyar Afirka a matsayin ƙasa mafi yawan jama’a, inda ƙasashe da dama ke kallonta a matsayin abin koyi na ƙarfi da zaman lafiya.
Ya kuma hori limaman da su ci gaba da wa’azi kan haɗin kai, haƙuri da zaman lafiya, tare da ƙarfafa mabiyansu su riƙa yi wa ƙasa da shugabanninta addu’a.
Gwamna Buni ya tunatar da ‘yan ƙasa cewa babu wata ƙasa da suke da ita face Najeriya, don haka wajibi ne su haɗa kai wajen kare makomar ta.
Mai Bai Wa Gwamna Shawara kan Harkokin Addini, Babagana Malam Kyari, ya bayyana taron a matsayin mai matuƙar muhimmanci, yana mai yaba wa haɗin kai da fahimtar juna da ke tsakanin malaman addini a jihar.
Ya ƙara da cewa mataki na gaba na wannan shiri zai haɗa da fastoci da shugabannin majami’u domin tabbatar da haɗin kai tsakanin addinai.
A nasu ɓangaren, limaman da suka halarta sun yi alƙawarin isar da saƙon zaman lafiya da haɗin kai ga mabiyansu, tare da tabbatar da ci gaba da yi wa Najeriya, shugabanninta da kuma al’umma addu’o’i domin samun ɗorewar zaman lafiya da ci gaba.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukumar Potiskum.