




Shekara shidan Gwamna Buni a fannin kasuwanci, noma, da masana'antu
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
4 days ago
Yayin da gwamnatocin jihohi ke bikin cika shekaru shida/biyu kan karagar mulki, na yi nazari kan tasirin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, kan harkokin kasuwanci, noma, da masana’antu da za su iya farfado da tattalin arzikin jihar Yobe.
Jihar Yobe jiha ce mai arzikin kasuwanci, noma, da masana’antu, Gwamna Buni ya taka rawar gani wajen daidaita tattalin arzikin jihar da samar mata da gogayya da takwarorinta a fadin Najeriya da samar da tsarin kasuwanci na zamani wanda zata iya gogayya da ‘yan kasuwa a fadin duniya.
A cikin shekaru shida na mulkin Gwamna Buni, ya samar da kasuwannin zamani guda bakwai masu inganci, wadanda suka zama kasuwannin da za su iya gogayya da manyan kasuwannin duniya a kananan hukumomi bakwai daban-daban na jihar: Potiskum, Geidam, Damaturu, Nguru, Yunusari, Gashua, da Ngalda na kananan hukumomin Fika da Bade.
Tasirin su zai zamanantar da harkokin kasuwanci, fadada hada-hadar kudi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, da jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje su zo su zuba jari a cikin kasuwancinmu, karfafa hanyoyin shiga da fita, da fadada haraji ga kananan hukumomi, kungiyoyin ‘yan kasuwa, da jihar Yobe.
Haka kuma gwamnatinsa cikin shekaru shida ta farfado da tsofaffin masana’antu, sannan ta dawo da martabar ma’aikatun jihar, sannan ta gina wasu kamfanoni guda shida masu suna “Sesame Brittle Processing Companies” wadanda za su yi matukar tasiri wajen inganta tattalin arziki da samar da dubban ayyukan yi a fadin jihar. Garuruwan da suka ci gajiyar sabbin masana’antun sun hada da Potiskum, Damaturu, Machina, da Nguru Sesame Brittle Processing Company.
Tasirin da suke da shi shi ne karfafa gwiwar manoma, da habaka sana’ar noma, samar da ayyukan yi ga dubban mazauna Yobe, da kuma jawo hankalin masu zuba jari ga sana’ar rid'i a jihar, domin a yanzu kamfanonin suna da karfin sarrafa su da kuma tattara rid'in, ta yadda daga jihar Yobe, ‘yan kasuwa za su iya fitar da shi kai tsaye zuwa kasashen waje, kuma hakan zai kara samun kudaden shiga ga kananan hukumomi da gwamnatin jihar Yobe.
A cikin shekaru shidan da suka gabata Gwamna Buni ya samar da damammakin noma iri-iri ga manoman rani da damina domin karfafa noma, samar da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin jihar Yobe. Sama da manoma 5,000 ne ke cin gajiyar aikin noma duk shekara a karkashin shirin gwamnatinsa na “Mega Agricultural Empowerment”.
Ko a bana, ya karfafa ofisoshin ayyukan raya aikin gona na shiyya da kayan aikin noma na zamani wadanda ke da tasiri wajen zamanantar da aikin noma da suka hada da taraktoci, injinan tono, da na’urorin noma na zamani iri-iri.
Har ila yau, a shekarar da ta gabata a cikin watan Yuli, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona mafi girma kuma mafi inganci a yammacin Afirka, wanda aka yi wa lakabi da "Yobe Multi-billion Agricultural Empowerment."
Empowerment din ya haɗa da tarakta 100, garman shanu 300, taki buhu 20,000, injunan shuka 1,349, injuna masu girbi 8,000, injinan garma na hannu 889, injinan ruwa mai amfani da hasken rana 4,000, famfunan ruwa 8,000, masu shukar hannaye 400. Injunan noma 4,000, Injunan girbi 8,000, magungunan kashe kwari, babura 200 na jami’an tsawaita aikin gona, motocin Hilux guda 7 na ofisoshin shirye-shiryen bunkasa noma na shiyya, injunan sara sama da 1000, da dubunnan buhunan iri iri-iri.
Tasirin wadannan ayyuka ya wuce yanzu; jihar za ta ci gaba da cin moriyarsu ta fuskar bunkasar tattalin arziki tsawon shekaru masu zuwa.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.


















