

Muna kashe kudi daidai da lalitar gwamnati, bamu ciwo bashi ba kuma bamu tsawwala haraji ba—Gwamna Buni
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
3 days ago
... Ya shelanta cewa damuwar su shine farfado da jihar da sake gina ta biyo bayan tabarbarewar al'amura sakamakon rikicin Boko-Haram.
.
.
The executive governor of Yobe State, Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, ya tabbatar da cewa duk da tarin ayyukan cigaba da gwamnatin sa takeyi Amma bata ciwo bashi ba kuma bata tsawwala wa al'ummar jihar kan biyan haraji ba.
Gwamnan yace har yanzu Yan kasuwan jihar Yobe basu gama farfadowa daga irin koma bayan da suka samu shekarun baya biyo bayan tashe tashen hankula da asarar da rikicin Boko-Haram ya haifar wa al'ummar jihar ba, wanda hakan ya raunata tattalin arzikin su da tattalin arzikin jihar gaba daya.
Gwamnan yayi wannan jawabin ne ga manema labarai yayin da yake zantawa dasu a ranar bikin cikar sa shekaru shida a Mulki ranar 29th, May, 2025.
"Duk da irin manya-manyan ayyukan da muka gudanar tsawon shekarun nan gwamnatin mu bata ciyo bashi daga gida ko wajen najeriya ba kuma bamu tsawwala haraji akan Yan kasuwannin mu ba Saboda har yanzu Yan kasuwan basu gama farfado wa daga koma bayan da suka samu sakamakon rikicin Boko-Haram ba.
"Muna daidaita ayyukan kashe kudi ne da Lalitar jihar mu. Mun gwammaci muyi aiki wa jihar mu da gwargwadon abinda muke dashi a asusun mu ba tare da Kakaba mata bashi ko tsawwala wa 'yan kasuwan mu ba," inji Shi.
Wannan Rawar Gani da Gwamna Buni yake takawa na kiyaye tattalin arzikin jihar da kawo ayyukan cigaba shine yakai shi ga samun nasarori da dama tare da baiwa gidauniyar Bankin Duniya ta (SFTAS) damar bashi lambobin yabo da karfafa jihar Yobe da kyaututtuka.
Koh a shekarar 2022 (STAS) din sun sanya jihar Yobe a sahun jihohin da ta kere tsakanin jihohi 36 game da dakile bashi da kuma rage bashin.
Mal. Ibrahim M. Nura
Special Assistant on Information and Communication to the Executive Chairman of Potiskum Local Government Area.


