
“Ina Nan Daram a APC”—Sanata Bomai Ya Karyata Jita-Jitar Sauya Sheka, Ya Tabbatar da cewa Yana Nan Daram A Jam'iyyar
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
18 days ago
Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu, Sanata Ibrahim Mohammed Bomai, ya sake fito wa fili domin musanta jita-jitar da ke cewa yana da niyyar ficewa daga Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai jaddada cikakken biyayyarsa da goyon bayansa ga jam’iyyar.
Sanatan ya bayyana hakan ne dangane da taron da wasu daga cikin masu neman kujerar gwamna a APC suka gudanar a Abuja, inda ya ce taron an shirya shi ne kawai domin karfafa hadin kai da kuma jaddada bukatar adalci, daidaito da samar da dama iri daya ga dukkan ‘yan takara a zaben fidda gwani mai zuwa.
A cewarsa, taron ya kuma mayar da hankali ne kan muhimmancin bin doka da ka’idoji kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa da dokar zabe suka tanada, domin tabbatar da gaskiya da sahihancin zaben cikin gida na jam’iyyar.
Ya bayyana rade-radin da ke cewa taron wata hanya ce ta shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, musamman ADC, a matsayin karya tsagwaronta da ba ta da tushe, yana mai cewa irin wadannan labarai na kokarin kawo rudani ne a siyasar jihar.
“Babu wani batun ficewa daga APC. Ina nan daram a jam’iyyar, kuma zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga manufofinta,” in ji Sanata Bomai.
Sanatan ya kuma tuna da irin rawar da ya taka tun bayan shigarsa APC a shekarar 2019, inda ya ce sun yi aiki tukuru wajen bunkasa jam’iyyar a yankin Yobe ta Kudu, wanda hakan ya kai ga samun nasara mai girma a zabukan 2019.
Ya kara da cewa a zaben 2023, APC ta sake nuna karfinta a jihar, inda ta yi nasara a kusan dukkan mukamai, sai dai kujera daya tilo da PDP ta samu da kyar.
Sanata Bomai ya yi kira da a tabbatar da gaskiya da adalci a zaben fidda gwani mai zuwa, yana mai jaddada cewa wajibi ne a bai wa dukkan ‘yan takara dama iri daya ba tare da kakaba wani ko nuna son kai ba.
Dangane da batun maslaha, ya ce duk wani tsari dole ne ya kasance a bude, mai gaskiya, tare da hada dukkan ‘yan takara da masu ruwa da tsaki domin kare hadin kan jam’iyyar da kuma tabbatar da nasara a zabukan gaba.
A karshe, Sanatan ya sake jaddada cikakken goyon bayansa ga APC, tare da kudirin ci gaba da aiki tukuru bisa gaskiya, adalci da rikon amana domin cigaban jam’iyyar da al’ummar Jihar Yobe baki daya.
Mal. Ibrahim M. Nura
Special Assistant on Information and Communication
Office of the Executive Chairman Potiskum Local Government Area.