

Hon. Salisu Muktari ya jagoranci taron kwamitin aiki kan NIPDs...ya bada tabbacin ci gaba da tallafawa lafiya
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
21 days ago
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya jagoranci taron Task Force on National Immunization Program Desks (NIPDs) tare da bada tabbacin ci gaba da bada goyon baya ga hukumar lafiya ta Potiskum LGA.
Taron dai an yi shi ne a shirye-shiryen fara aikin rigakafi na kwanaki takwas, wanda za a gudanar da shi a matsayin kamfen na kwana biyu a jere, da kamfen na kwana hudu gida-gida, da kuma kwanaki biyu.
A yayin taron kodinetan kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Potiskum Abdulrahman Musa ya tabbatar da cewa:
“Muna godiya ga mai girma shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari bisa goyon bayan da ya ba mu don tabbatar da jin dadin ma’aikatanmu da kuma taimaka mana a duk lokacin da muke bukata.
“Muna samun gagarumar nasara da ke nuna cewa muna kan hanyar samun nasarorin da ake so a fannin kiwon lafiya ba a jihar Yobe kadai ba har ma a Najeriya baki daya domin ko a watan jiya karamar hukumarmu ta yi nasarar yi wa yara 300,398 allurar rigakafi.
“Wadannan yara sama da dubu dari uku da aka yi wa allurar rigakafi a karkashin gundumomi 10 na karamar hukumar Potiskum, dukkansu ‘yan kasa da shekara 5 ne, kuma muna da burin ganin mun samu juriya 0% a karkashin yara ‘yan shekara 5 a zagaye na gaba." Inji shi
Taron ya samu halartar wakilan hukumar WHO, sarakunan gargajiya, hakimai, da sauran manyan baki, inda dukkansu sun yabawa mai girma shugaban bisa jajircewarsa na ba da fifiko kan kiwon lafiya a karamar hukumar Potiskum.
“Na ji dukkan bukatu da nasarorin da kuka samu a bangaren kiwon lafiyarmu, a shirye nake na ci gaba da ba ku hadin kai da gudumawa ta musamman don inganta ayyukanku.
“Ina rokon alfarmar ku da ku ci gaba da yin hakuri da jawo hankalinmu a duk inda kuke ganin ya kamata hankalinmu ya kasance, domin yana da kyau mu yi aiki tukuru don inganta rayuwar al’ummar kananan hukumominmu musamman a bangaren lafiya." A cewar Hon. Salisu Muktari
Wakilan WHO, da sarakunan gargajiya, da sauran su sun yaba masa bisa samar da ingantattun wuraren ajiyar kankara a cikin mai sanyi na PHC, wanda hakan wani shiri ne da ya inganta ayyukansu kai tsaye.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.





























1 day ago