Hon. Salisu Muktari Ya Jaddada Goyon Bayansa ga Matasa da Mata, Ya Daidaita Manufarsa Dana Gwamna Buni Na Karfafa Matasa A Harkokin Mulki
Potiskum LGA Eyes
Image

Hon. Salisu Muktari Ya Jaddada Goyon Bayansa ga Matasa da Mata, Ya Daidaita Manufarsa Dana Gwamna Buni Na Karfafa Matasa A Harkokin Mulki

Potiskum LGA Eyes
@muhammadnuraibrahim848393

7 days ago

Shugaban Karamar Hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya sake jaddada cikakken goyon bayansa ga manufofin haɗin kai na Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, CON, musamman wajen karfafa matasa da mata a harkokin mulki da shugabanci don dorewar cigaba.

Yayin jawabi a Sakatariyyar Karamar Hukumar Potiskum, Hon. Muktari ya jaddada cewa matasa da mata sune ginshiƙai wajen gina al’umma mai albarka, ya bayyana su a matsayin “injinan kirkire-kirkire da ginshiƙan cigaban al’umma”, yana mai cewa babu wata al’umma da za ta cimma nasara idan aka yi watsi da wadannan rukuni biyu.

Ya yabawa Gwamna Buni bisa samar da dama ta musamman da ke baiwa matasa da mata damar shiga a mukaman shugabanci, yana mai cewa irin wannan mataki ya canza tsarin mulki a Jihar Yobe, kuma ya zama abin koyi ga sauran jihohi.

Don karfafa fata, Hon. Muktari ya kawo misalin farfesa mace ta farko a fannin likitancin dabbobi a Najeriya—wadda asalin ’yar Potiskum ce—a matsayin shaida ta cewa mata na iya cimma manyan matsayi idan aka tallafa musu yadda ya kamata.

Ya kara da cewa irin wannan gagarumin nasara ya kamata ya zama abin koyi ga matasa su dage wajen neman ilimi, shugabanci, da hidima ga al’umma.

“Gwamna Buni ya shimfida tubalin hadin kai, kuma mu a matakin kananan hukumomi dole mu ci gaba da gina wannan gini, mulkinmu zai ci gaba da bude kofar dama ga matasa da mata domin shiga cikin harkokin mulki, siyasa da cigaban al’umma, tare za mu tabbatar da cewa cigaba ya taba kowace gida da kowane dan kasa,” in ji Hon. Muktari.

Shugaban ya tabbatar da cewa Karamar Hukumar Potiskum za ta ci gaba da kasancewa kan tafarki da tsari irin na Gwamna Buni wajen inganta ayyukan matasa, karfafa mata a dukkan matakai, tare da aiwatar da manufofin da ke tabbatar da adalci, kirkire-kirkire da hadin kai.

Mal. Ibrahim M. Nura
SA Information and Communication ga Shugaban Karamar Hukumar Potiskum

216
3280
3
7 days ago

Roane Bailee Hall Nicole Zukowski Jeffrey Scholten Brendan Vallejos Judah Robinson Jase Mitchell Maggie Griffey Nash Martin Jonas King Niklaus Perez Uriel Ross Alena Watson Jacoby Taylor Mary Ross Itzayana Blas Joelle

Sign in to post a comment.


Sign In


User Profile
Roane Theo @theoroane1182
Hey there! Just reading through this, seems like a bunch of local heroes keeping things running smoothly. Karamar Hukumar Potiskum looks like a real asset, and Gwamna Buni's dedication is top-notch. Can't wait to see what else they're up to.
2 days ago

User Profile
Ping Louise @louiseping3491
Haha, seems like another political update from our community leaders! Gwamna Buni and Hon. Muktari ya jaddada, always doing their bit for the region. Don karfafa fata, don't miss it if you're around!
1 day ago

User Profile
Abe Marilyn @marilynabe8224
Wow, congratulations to all of you! Hope this new title means more success ahead.
1 day ago