Bamu da hanun jarin da ya fi ilimi, dole ne mu inganta shi kuma mu tabbatar da shi ga jama’armu.—Hon. Salisu Muktari Ga LEA
ibrahim muhammad nura
Image

Bamu da hanun jarin da ya fi ilimi, dole ne mu inganta shi kuma mu tabbatar da shi ga jama’armu.—Hon. Salisu Muktari Ga LEA

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

5 days ago

Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya tabbatarwa hukumar ilimi ta karamar hukumar Potiskum cewa ita ce ke da alhakin kawo sauye-sauye domin inganta ilimi domin bamu da hanun jarin da ya wuce ilimi.

Chairman din ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake duba aikin gina ajujuwa da ake yi a makarantar firamare ta Buraima da ke karamar hukumar Potiskum, inda ya ba da tabbacin cewa dole ne hukumomin da ke da alhakin ilimi su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingancinsa.

“Ku ne ke da alhakin kawo sauye-sauye a fannin ilimi, kuma dole ne mu hada karfi da karfe wajen tabbatar da ingancin ilimi a wannan karamar hukuma.

“Mu fada wa kanmu gaskiya, mu tashi tsaye mu samar da al’ummar da za mu yi alfahari da ita a nan gaba, domin hakkinmu ne samar da ingantaccen tsarin ilimi ga al’ummarmu.

“Kofarmu a bude take a kodayaushe domin tuntuba ko bayar da duk wata gudunmawa da za ta tabbatar da ingancin ilimi a kokarinmu na tabbatar da aniyar gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin mai girma Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, kan harkokin ilimi." Hon. Salisu Muktari ya fadawa E.S Potiskum LEA.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa Gwamna Buni ya taka rawar gani wajen ganin an samar da tsarin zamani a fannin ilimi a daukacin kananan hukumomi 17 na jihar Yobe, kuma ya rage gare mu mu kula da tsarin.

“Gwamna Buni ya taka rawar gani wajen inganta ilimi, abin da ya rage mana shi ne kiyaye tsarin saboda ba mu da jarin da ya fi ilimi tasiri ga rayuwarmu." Ya kara da cewa.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

88
1326
5 days ago

Ross Kyree Vallejos Kaylee Symons Denisse Martin Aliana Lopez Alison Griffey Nash Ramos Karson Long Jedidiah Roberts Ronan

Sign in to post a comment.


Sign In