WHO, Melinda Gates, PHC Board, da Potiskum Emirates Council sun yaba wa Hon. Salisu Muktari kan tallafawa fannin lafiya
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

WHO, Melinda Gates, PHC Board, da Potiskum Emirates Council sun yaba wa Hon. Salisu Muktari kan tallafawa fannin lafiya

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

19 days ago



Hukumar lafiya ta duniya (WHO), Melinda Gates, hukumar kula da lafiya matakin farko na karamar hukumar Potiskum (PHC), da majalisar masarautar Potiskum sun yabawa shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, bisa tallafawa fannin kiwon matakin farko.

Wakilan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Majalisar Masarautar Potiskum da Melinda Gates sun yaba masa ne a yayin da suke gabatar da jawabin godiya ga shugaban yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar lafiya a dakin taro na sakatariyar karamar hukumar Potiskum a ranar Talata 10 ga watan Yuni 2025.

“Muna yabawa mai girma shugaban karamar hukumar bisa jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’umma da kuma farfado da harkokin kiwon lafiya matakin farko a wannan karamar hukumar.

“Tabbas duk nasarar da karamar hukumar Potiskum ta samu a fannin kiwon lafiya na da alaka kai tsaye da jajircewar shugaban karamar hukumar na ganin an cimma burin karfafa rayuwar al’umma ta hanyar kiwon lafiya matakin farko.

“Muna godiya da irin kwarin gwiwa da kwarin gwiwarka mai girma chairman, kuma muna sake mika godiyarmu bisa irin goyon baya da kwarin gwiwa da kake baiwa ma’aikatan lafiya a wannan karamar hukumar domin dukkanmu mun san cewa kofarka a bude take a kodayaushe domin karfafa ayyukan kiwon lafiya da kuma tabbatar da cewa sun samu ingantaccen tsari." A cewar wakilin WHO.

Haka kuma Majalisar Masarautar Potiskum ta bakin mai kula da harkokinsu Alh. Muhammad Gambo (Zarman Potiskum), ya nanata jin dadin su bisa yadda Honorabul Chairman yake Kula da gudanar da ayyukan kiwon lafiya a karamar hukumar Potiskum.

“A madadina da mai martaba Sarkin Potiskum, muna yabawa tare da nuna jin dadinmu da kokarin mai girma shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari na karfafa ma’aikatan lafiya a matakin farko a wannan karamar hukumar.

“Alkawarinsa ya yi daidai da manufofin bunkasa kiwon lafiya a duniya, mun gamsu da kokarin da yake yi na farfado da kiwon lafiya domin a yanzu mun samu nasarorin da ke nuni da cewa muna kan gaba wajen inganta kiwon lafiya a fadin Najeriya ba wai a jihar Yobe kadai ba." Inji Shi

Chairman din ya kuma sadaukar da wannan yabo ga amininsa kuma gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN.

“Na sadaukar da dukkan wannan yabo da godiya ga mai girma Gwamna Hon. Mai Mala Buni FCIA CON COMN domin ta hanyar jajircewarsa da kokarin gwamnatinsa na tabbatar da manufofin inganta kiwon lafiya ya sa muke taka muhimmiyar rawa wajen ganin an aiwatar da tsare-tsare da za su amfanar da al’umma." A cewar Hon. Salisu Muktari

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

181
2722
1
19 days ago

Kim Jad Garzon Estella Hill Brody Ping Kinslee Collins Otis Parker Danielle Mcelrath Arjun Symons Denisse Hall Juelz Howard Emir Moore Yara Fiorentino Everlee Collins Lennon Peay Kyree Baker Damien Rodriguez Victor

Sign in to post a comment.


Sign In


User Profile
Rothenberg Jagger @jaggerrothenberg7058
Wow, this international collaboration sounds amazing! Rafamycin has the potential to save countless lives. I hope they overcome any challenges and continue working together so well.
5 days ago