




Tinubu, Atiku, Obi, da Jonathan: Sabon Hali da Canji a Hasashen Siyasar Najeriya, PDP Na Neman Sauya Fuskar Siyasar 2027 Biyo Bayan Mika Tikitin Kudu
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
4 days ago
Tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP zuwa Kudu zai dawo da tasirin siyasar Arewa a 2027 ko kuwa farkawa ne ga jam'iyyar APC don gyara rikice-rikicen da take fuskanta Arewar don fuskantar zaben 2027 da kwarin gwiwa da gaskiya?
A yau an samu wani yunkuri daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP wanda zai iya nuni da makomar siyasar 2027 da kuma bayyana irin damar da Arewa da jiga-jigan siyasar Arewa za su samu gurin tafiyar da tsarin mulkin dimokuradiyya da kwarewa idan ‘yan siyasar Arewa suka amince, su ka kuma fuskanci hadin kai a 2027.
Jam’iyyar siyasa mafi dadewa kuma babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP mai adawa da jam’iyya mai mulki a siyasance da kuma jam’iyyar hadaka ta ADC wadda a halin yanzu ke shirin hada kai don tsayar da Dan takara a zaben shekarar 2027, a hukumance sun bayyana aniyarsu ta bai wa yankin kudancin Najeriya tikitin takarar shugaban kasa kai tsaye, wanda hakan ya bai wa yankin kudancin kasar damar tsayar da ‘yan takara 3 masu tasirin fada aji a Yankin.
A cewar matakin da PDP ta dauka, kasancewar ta jam’iyyar da tafi kowace jam’iyya tasiri a jam’iyyar adawa, kai tsaye ta bai wa yankunan siyasar kudancin Najeriya guda uku, wato Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma, da Kudu maso Gabas ‘yancin tsayar da dan takarar shugaban kasa, lamarin da ya tabbatar da rade-radin da ake yi na cewa tsohon shugaban Najeriya Dakta Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takarar shugaban kasa, wanda jam’iyyar ta dade tana neman sa don sake neman shugaban kasa da aka dade ana rade-radin cewa jam’iyyar tana da shirin bashi takara a babban zaben 2027.
A daya hannun kuma, idan jam’iyyar ADC da Peter Obi na LP, wadanda ke da tasiri mai karfi a siyasar kudancin kasar, ba za su iya kulla kyakyawar alaka da dunkulewa a jam’iyyar ADC ba, yankin kudancin kasar na da kyakkyawar damar sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyarsu ta Labour Party (LP), wanda hakan zai sake baiwa yankin kudancin kasar damar tsayar da dan takara mai karfi da zai yi barazana ga tasirin siyasar yankin kudu da kuma raba kuri’u.
Idan aka yi la’akari da cewa jam’iyyar APC mai mulki ta dade da ayyana shugaban kasa mai ci Asiwaju Bola Ahmed Tinubu GCFR a matsayin dan takararta na din-din-din a zaben 2027, ana ganin cewa a yanzu yankin kudancin kasar na da damar tsayar da ’yan takara uku masu karfi da tasiri a lokaci guda a zaben 2027, inda daukacin kuri’un kudancin kasar za su rabu gida uku ga 'yan siyasar uku masu tasiri daga yankin.
A gefe guda kuma, jam’iyyar ADC ta samu shiga a yankin arewa biyo bayan al'ummar yankin na ganin ana ware su gurin rabon mukami da gudanar da ayyukan cigaba inda muryar dan adawa kuma gogaggen dan siyasa daga Arewa, wanda ya taba zama mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa har sau biyu daga 2007 zuwa 2023, ya sha alwashin zama dan takara a karkashin jam’iyyar ADC din daga Arewa.
Ya zuwa yanzu, a matsayin jam’iyyar ADC mai taken “Hadaka”, babu wani tabbaci na tsayawa takara ko tikitin takarar shugaban kasa, duk da cewa daga yankin Arewa, muryar Atiku Abubakar ce ta fi yin tasiri a yanzu duk kuwa da cewa Arewa ce ta fi kowace yanki yawan kuri’u da yawan al’umma a Najeriya.
A bangare guda kuma ana kallon Kwankwaso a matsayin wanda zai zama tarnakin gaske ga takarar Atiku Abubakar a Arewa, kasancewar shi jigo ne a jam’iyyar NNP, kuma shi ne ke rike da shugabancin siyasar Jihar Kano, jiha ce kuma mai matukar tasiri da kuri’u a siyasar Arewa.
Kalaman da suka fi daukar hankali sun tabbatar da yiwuwar Kwankwaso ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa na daya daga cikin ‘yan takarar da za su fito daga Kudu a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, wanda idan har aka tabbatar da hakan zaiyi tasiri ne ga shafin PDP da dan takararta, Goodluck Jonathan ba ga makomar siyasar Arewacin Najeriya ba.
Arewa tana da matukar tasirin yawan jama’a da yawan kuri’u. Idan har jam’iyyar APC da sauran Jam’iyyun siyasa suka tunkari 2027 a cikin wannan hali, to babu makawa tasirin jam’iyyar ADC da dan takararta, Atiku Abubakar a zaben 2027 tabbatacce ne, domin shi ne dan takara daya tilo daga yankin Arewa da ke ikirarin ana nuna wa wariya a halin yanzu saboda tsarin mulki da rigingimun bangaranci a karkashin jam’iyya mai mulki.
Idan har jam’iyyar APC ta bar kanta ta shiga cikin zafafan lokacin siyasa a haka ba tare da magance wutar rikicin bangaranci da ke addabar jam’iyyar a yanzu da kuma gyara nuna wariya ga wasu yankunan Arewa ba, Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta ADC suna da damar samun kashi 75% na kuri’un Arewa a matsayin sa na dan takarar shugaban kasa daya tilo daga yankin.
Idan ya samu kashi 75 cikin 100 na kuri’un Arewa, zai iya samun kashi 15% daga Kudu, sai sauran ‘yan takara uku daga Kudu su raba kashi 85% na kuri’un yankinsu, sauran kashi 25% daga Arewa kuma suyi warwason shi.
Har yanzu akwai dimbin damammaki ga jam’iyyar APC mai mulki don waiwaya wa baya, ta gyara kura-kuran ta kafin lokaci ya kure.
Mal. Ibrahim M. Nura
Dan jarida, dan siyasa, kuma manazarcin siyasa daga arewa maso gabashin Najeriya.




























