Mun kirkiro wani tsari don saukaka sake tsugunar da 'yan gudun hijra da suka rasa matsugunansu –Gov. Buni ya fadawa IOM
ibrahim muhammad nura
Image

Mun kirkiro wani tsari don saukaka sake tsugunar da 'yan gudun hijra da suka rasa matsugunansu –Gov. Buni ya fadawa IOM

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

16 days ago



Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, ya tabbatar wa tawagar IOM cewa gwamnatinsa ta samar da wani tsari da zai inganta rayuwar al’umma tare da saukaka tsugunar da ‘yan gudun hijira a fadin jihar Yobe.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata ganawa ta hadin gwiwa da kungiyar ta IOM, inda DG Press and Media Affairs na Mai Girma Gwamna Mamman Mohammed ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye take ta hada kai, amma babu wani sansanin ‘yan gudun hijira da ya rage a fadin jihar Yobe.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa ta ware kashi 5.0 cikin 100 na kasafin kudin bana domin inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da samar musu da ababen more rayuwa.

“Mun yi farin ciki da wannan haɗin gwiwa, kuma ina tabbatar muku cewa gwamnatinmu ta ba da jari mai tsoka a fannin ilimi, noma, kiwon lafiya, hanyoyi, wutar lantarki, da ruwan sha don zamanantar da rayuwar al’ummarmu a ƙarƙashin wannan gwamnati.

“Na yi farin ciki da kwarin gwiwar ku na yin aiki tare da gwamnatinmu don taimaka wa rayuwar al’umma, ina kuma kara tabbatar muku da cewa ba mu da wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da suka rage a Jihar Yobe saboda mun sake tsugunar da su cikin aminci da mutunci, abin alfahari ne a gare mu.” Yace

A nasu bangaren, babban wakilin IOM ta kuma yabawa Gwamna Buni bisa jajircewarsa na ganin an magance matsalolin ‘yan gudun hijira a jihar Yobe.

“Muna matukar yaba muku kan kokarin da kuke yi na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira a Jihar Yobe, wannan ya nuna cewa kai shugaba ne mai zuciya ta musamman da kuma nuna matukar damuwa ga matsalolin da jama’a ke fuskanta bayan sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar cikin mutunci.” Sharon ta ce

Har ila yau, Sharon ta jaddada kudirin IOM na hada gwiwa da gwamnatin jihar Yobe domin inganta rayuwar al'ummar jihar Yobe.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

368
5526
16 days ago

Watson Malik Rivera Gideon Martinez Kellan Torres Genesis Stgeorge Lauryn Martinez Katie King Mckenna Gonzales Paris Murphy Colin Hausman Luisa Sanchez Kannon White Myles Price Bristol Griffey Nash Haga Jessie Bumpus Mckenna Cadet Jaiden Hill Brody Ross Alena Walker Braelynn Scholten Simon Murguia Monroe Pooler Felipe Million Rory Clark Helen Scholten Brendan Buhler Eloise Crowl Christian Buhler Jadiel Killeen Rohan Stewart Rosalie Socha Kyra Ramos Jacob Watson Jacoby Rodriguez Anya Jepson Mariam

Sign in to post a comment.


Sign In