Gwamna Buni na ci gaba da aikin gina Sabon titin Dumbulwa zuwa Lailai da magudanar ruwa a karamar hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Gwamna Buni na ci gaba da aikin gina Sabon titin Dumbulwa zuwa Lailai da magudanar ruwa a karamar hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

13 days ago

Gwamnan jihar Yobe, H.E. Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, a halin yanzu yana aikin gina Sabon titin/kwalta tare da magudanan ruwa wanda zai hade yankunan Dumbulwa da Lailai na karamar hukumar Potiskum.

Dumbulwa zuwa Lailai yanki ne da ke cikin karamar hukumar Potiskum wanda ke da karancin hanyoyin shiga kuma ya dade yana fama da karancin magudanan ruwa; gina wannan hanya da magudanar ruwa za su yi amfani da kuma samar da mafita ga dimbin matsaloli a yankin.

Duk da kasancewarsu a kusa, shiga juna yana da matukar wahala saboda rashin ingantaccen hanyoyin shiga, wanda hakan ya haifar da koma baya a fannin tattalin arziki, ilimi, kasuwanci, zamantakewa da al'adu na yankunan.

Aikin titin da mai girma gwamna yake yi a halin yanzu zai karawa mazauna yankin karfin gwiwa ta hanyar samar musu da saukin ilimi, kiwon lafiya, kasuwanci, noma da kuma farfado da martabar yankin saboda samun ingantaccen hanyar sufuri da saukin shiga da fita saboda ingantacciyar hanyar.

Gwamna Buni ya dauki matakin gina hanyoyin shiga da fice sama da 170 nan da shekarar 2025 a fadin jihar Yobe, inda ya yi alkawarin farfado da harkar sufuri, da inganta harkar noma, da kuma karfafa tattalin arzikin jihar Yobe, wanda yana daya daga cikin abubuwan da ke cikin kasafin kudin bana, mai taken “kasafin tattalin arziki da rage talauci.”

Nagartattun mutanen yankin sun bayyana farin cikinsu da jin dadin shugabancinsa. Mazaunin unguwar Alh. Umaru Potiskum, ya ce;

“Muna godiya, da farin ciki, da alfahari da samun wannan aikin hanyar domin gina wannan titin zai sauwaka mana abubuwa da dama, tun daga kiwon lafiya da ilimin yaranmu har zuwa harkokin kasuwanci”. Inji Shi

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

212
3187
13 days ago

Lopez Alison Backman Mira Hughes Royal Cheshire Ander Thoms Kylo Charleston Adaline Rodriguez Anya Reed Jeremias Brown Melvin Ramirez Amias Kelly Miles Cruz Santana Lucy Kennedi Edelstein Journey Erazo Adelina Harris Kimora Garzon Estella Hoeft Sarai Thomas Yaretzi Jackson Cameron Mcdavid Khloe

Sign in to post a comment.


Sign In