Dakile Ambaliya: Hon. Salisu Muktari Ya Na Ci Gaba Da Gyaran Magudanun Ruwa Da Yashe Su A Karamar Hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image

Dakile Ambaliya: Hon. Salisu Muktari Ya Na Ci Gaba Da Gyaran Magudanun Ruwa Da Yashe Su A Karamar Hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

3 days ago

... Yayin da damina ke ci gaba da karatowa, chairman din yana gyaran magudanan ruwa da domin dakile barazanar ambaliya.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, yana ci gaba da kwashe wa tare da gyara magudanun ruwa a fadin karamar hukumar Potiskum domin hana afkuwar ambaliyar ruwa.

Chairman din ya himmatu wajen inganta rayuwar al’umma tare da tabbatar da cewa an kawar da duk wani abu da zai kawo cikas ko kawo tsaiko ga al'ummar karamar hukumar; don haka ne a halin yanzu yake gyara tare da kwashe magudanar ruwa a fadin karamar hukumar.

Kamar yadda karamar hukumar Potiskum na cikin kananan hukumomin jihar Yobe da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da ke haddasa lalata gidaje, asarar dukiya, da asarar rayuka, wanda masana suka tabbatar da toshe hanyoyin ruwa (magudanar ruwa) shi ke haifar da afkuwan hakan a duk shekara.

Chairman din ya dauki matakin farko na magance matsalar ambaliyar ruwa ta hanyar gyara da kwashe magudanar ruwa a karamar hukumar Potiskum din.

Sannan ya kuma yi kira ga jami’an kula da muhalli na karamar hukumar da su inganta ayyukansu domin dakile duk wata barazana ta muhalli ga al’ummar karamar hukumar Potiskum tare da alwashin ba su cikakken goyon baya don inganta ayyukansu a kowane lokaci.

“Ina kira ga jami’an kula da muhalli na wannan karamar hukumar da su inganta aikinsu wajen sanya ido kan duk wani lamari da zai kawo cikas ga rayuwar al’ummarmu, tun daga matsalolin lafiya da matsalolin da suka shafi ambaliyar ruwa da sauran barazana daga duk wani abu da ka iya gurgunta zamantakewar al’ummarmu.

“A shirye muke da dukkan karfinmu don bayar da tallafin da ya dace don karfafa wa wannan fannin gwiwa domin inganta ayyukansu da inganta rayuwar al’ummarmu,” inji shi.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

75
1130
3 days ago

Crowl Christian Caffrey Otis Rodriguez Anya King Mckenna Lopez Alison Myers Daniela

Sign in to post a comment.


Sign In