


“Zamu Ci Gaba da Goyon Bayan Manufar Gwamna Buni Domin Gina Yobe Mai Zaman Lafiya da Cigaba.” — Hon. Salisu Muktari
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
12 days ago
Shugaban Karamar Hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da mara wa Gwamna Mai Mala Buni baya wajen aiwatar da manufofi da tsare-tsaren sa na gina Jihar Yobe mai cike da kwanciyar hankali, ci gaba, da haɗin kai.
Hon. Salisu Muktarin ya kuma jinjinawa Gwamna Buni bisa irin nagartaccen shugabanci da ya nuna, wanda ya mayar da hankali kan zaman lafiya, ci gaban al’umma, da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
“Zamu ci gaba da goyon bayan hangen nesa da manufar Gwamna Mai Mala Buni domin tabbatar da Yobe mai cike da zaman lafiya da ci gaba. Gwamnatinsa ta kawo sauyi, ta dawo da kwanciyar hankali, haɗin kai, da cigaba, kuma mu a Potiskum muna alfahari da kasancewa cikin masu tallafa masa daga matakin ƙananan hukumomi,” in ji Hon. Muktari.
Ya bayyana cewa Karamar Hukumar Potiskum na ci gaba da aiwatar da shirye-shirye da suka yi daidai da tsarin ci gaban gwamnatin jiha, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, hanyoyi, da inganta rayuwar matasa.
“Manufarmu ita ce ganin cewa dukkan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jiha sun iso ga jama’a kai tsaye, muna aiki tukuru domin tabbatar da cewa kowane ɗan ƙaramar hukumar Potiskum ya amfana da canjin da gwamnatin Gwamna Buni ke kawowa,” ya ƙara da cewa.
Hon. Salisu Muktari ya kuma yaba wa Gwamna Buni bisa shugabanci mai haɗa kan kowa da kowa, yana mai cewa irin wannan tsarin ne ya dawo mana da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummar jihar Yobe.
Ya yi kira ga jama’a, shugabannin gargajiya, da kungiyoyin matasa da su ci gaba da mara wa gwamnatin jiha baya, yana mai tabbatar da cewa Karamar Hukumar Potiskum zata kasance amintacciyar abokiyar haɗin kai wajen cimma burin gwamnatin jiha.
A karshe, ya kuma jaddada cewa Karamar Hukumar Potiskum zata ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen aiwatar da manufofin Gwamna Buni domin tabbatar da Jihar Yobe mai cike da kwanciyar hankali, ci gaba, da ɗorewar cigaban tattalin arziki.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mai Taimakawa Shugaban Karamar Hukumar Potiskum na Musamman kan Harkokin Bayanai da Sadarwa.





9 days ago

9 days ago

5 days ago

14 hours ago