Tsarin Gwamna Buni: Shugabannin Kananan Hukumomi 17 da Sarakunan Gargajiya Sun Zama Haske ga Adalci, Zaman Lafiya da Sabuwar Rayuwa a Yobe
Potiskum LGA Eyes
Image
Image
Image
Image

Tsarin Gwamna Buni: Shugabannin Kananan Hukumomi 17 da Sarakunan Gargajiya Sun Zama Haske ga Adalci, Zaman Lafiya da Sabuwar Rayuwa a Yobe

Potiskum LGA Eyes
@muhammadnuraibrahim848393

1 day ago

A yau, idan ka zaga lungu da sakon Jihar Yobe, za ka samu sabin tsaruka na cigaba da kwanciyar hankali, a karkashin Gwamna Mai Mala Buni, ana sake rubuta tarihin kananan hukumomi — daga matsayinsu na ofisoshi na gudanarwa, zuwa cibiyoyi na gaskiya da ke sauya rayuwar al’umma.

Tsare-tsaren Gwamna Buni ta janyo sabuwar tafiya ta shugabanci inda shugabannin kananan hukumomi 17 suka koma wakilan canji, suna aiki da sarakunan gargajiya da ke da karfin al’umma da darajar adalci, wannan haɗin kai ya sake farfaɗo da amincewar jama’a ga gwamnati, ya kuma ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a gundumomi 178 na jihar.

Karkashin Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, ayyuka suna fitowa fili a dukkan yankuna, a karamar hukumar Fune da Nangere, sabbin hanyoyi sun haɗa manoma da kasuwanni, suna sauƙaƙa musu kai amfanin gona akan lokaci hakanan a Gulani da Tarmuwa, cibiyoyin lafiya sun bunkasa, suna taimaka wa mata da yara su sami kulawar likita a kusa da su.

A Potiskum da Geidam, shirye-shiryen ƙarfafa matasa da mata na buɗe sabbin hanyoyin dogaro da kai, yayin da rijiyoyin burtsatse da famfuna a Jakusko, Machina da Karasuwa ke samar da ruwan sha mai tsafta da sauƙi ga kauyuka da dama.

“Jagorancin Gwamna Buni ya tabbatar da cewa ci gaba na hakika yana farawa daga ƙasa,” in ji wani jami’i na ma’aikatar. “Ya haɗa gwamnati da sarakuna cikin kawance na gaskiya wanda ke samar da zaman lafiya da amincewa.”

Ga jama’a, wannan canji ba magana ba ne kawai — abune na zahiri da gani a ido. Malam Audu, manomi daga Fika, ya ce: “A da ba mu da hanya, yanzu muna kai amfanin gona kasuwa cikin sauƙi. Muna ciyar da iyalanmu cikin alfahari.” Fatima, mai dinki daga Tarmuwa, ta ce: “Da tallafin gwamnati, na kafa sana’a ta. Yanzu ina rayuwa cikin mutunci, ina kula da ’ya’yana da farin ciki.”

Yanzu, sarakunan gargajiya sun dawo da martabar su a matsayin ginshiƙai na zaman lafiya, masu sasanta rikice-rikice da ɗora al’umma kan hanyar da ta dace.

A yau, kananan hukumomin Yobe sun zama cibiyoyin hidima, inda shugabanni ke jagoranci da hangen nesa, sarakuna ke ba da hikima, al’umma kuma ke jin tasirin mulki kai tsaye.

Tushen Farkawar Gwamna Mai Mala Buni ya wuce manufa — tsarine mai kyau na adalci, zaman lafiya da sabuwar rayuwa, wanda aka gina daga ƙasa zuwa sama.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mai Taimakawa Shugaban Karamar Hukumar Potiskum Shawara na Musamman kan Harkokin Labarai da Sadarwa.

52
783
1 day ago

Collins Lennon Myhre Dylan Mcclean Whitley Corry Royce

Sign in to post a comment.


Sign In