Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Gwamna Buni: Jihar Yobe Ne Ta Farko a Saukin Rayuwa Kamar Yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana
Potiskum LGA Eyes
Image

Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Gwamna Buni: Jihar Yobe Ne Ta Farko a Saukin Rayuwa Kamar Yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana

Potiskum LGA Eyes
@muhammadnuraibrahim848393

13 days ago

... Kididdiga ta NBS ta tabbatar da cewa jihar Yobe ita ce jiha mafi Saukin Rayuwa ga mazaunanta a Najeriya.


Jihar Yobe karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Hon. (Dr.) Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ta kasance jiha mafi Saukin Rayuwa a Najeriya kamar yadda kididdigar NBS ta nuna.

Hakan ya samu ne sakamakon tsare-tsare da gyare-gyaren tattalin arziki da mai girma Gwamnan Jihar Yobe Hon. (Dr.) Mai Mala Buni FCIA CON COMN, ta samar don saukaka rayuwa da habaka tattalin arzikin jihar Yobe.

Daga cikin manyan tsare-tsare da gwamnatin jihar Yobe ta yi na samar da sauki ga al’ummarta, har da saukaka haraji domin gwamnatin jihar Yobe ba tsawwala haraji ba don kula da farashin kayan masarufi da samar da kasuwanci mai inganci da rahusa ga al’ummarta.

Gwamnatin jihar ta kuma samar da ingantattun tsarin inganta noma na zamani tare da himmantuwa wajen tabbatar da cewa noma ya sauya fasali daga sana’ar hannu zuwa kasuwanci mai riba tare da samar da dogaro da kai ga mazauna jihar.

Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin mai girma gwamna Hon. (Dr.) Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ta kuma samar da hanyoyin taimakawa kananan ‘yan kasuwa da jari tare da samar da wuraren lamuni marasa riba domin inganta rayuwar al’umma da samar da ayyukan yi.

Sakamakon hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ya tabbatar da cewa jihar Yobe ita ce ta daya a saukin rayuwa, yayin da jihar ke kan gaba wajen dakile hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda ya fadi da 2.8% a watan Yuli.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

114
1746
13 days ago

Reed Jonas White Myles Jepson Paislee Martinez Marcel Howard Kailey Patel Orion Moore Yara Stewart Everett Williams Valentina Gonzales Chelsea Collins Ellie Myhre Dylan

Sign in to post a comment.


Sign In