

Shirye-shirye biyu na Gwamna Buni da ke nuna aniyarsa na inganta rayuwar al’ummar karkara a fadin Jihar Yobe
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
3 days ago
... samar da ingantaccen wutar lantarki a kauyuka da samar da hanyoyin shiga karkara guda 178.
•
•
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, ya himmatu wajen inganta rayuwar mutanen karkara ta hanyar samar musu da ingantaccen wutar lantarki da isassun hanyoyin shiga da za su hada su da garuruwan jihar Yobe cikin sauki.
Kamar yadda kowa ya sani gwamnatin jihar Yobe ta himmatu wajen samar da hanyoyi guda 178 da za su hade gundumomi 178 na jihar da garuruwan jihar, wanda hakan na daga cikin kudiri/aniya mafi inganci da gwamnan ya sanya a cikin kasafin kudin shekarar 2025.
Wani sabon babi da ya ja hankali wajen inganta rayuwar mutanen karkara shi ne, a jiya gwamnatin jihar Yobe ta hada gwiwa da gwamnatin tarayya wajen samar da wadataccen wutar lantarki ga al’ummar da ke zaune a kauyukan jihar Yobe.
A yayin da aka rattaba hannu da yarjejeniyar fahimtar juna a ranar Alhamis 26 ga watan Yuni, 2025 a Abuja, wanda ya hada gwamnatin jihar Yobe, da hukumar samar da wutar lantarki ta yankunan karkara (REA), da masu ruwa da tsaki a fannin makamashin Najeriya.
Tuni dai gwamnatin jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a fannin samar da wutar lantarki, inda ta samar da wutar lantarki a wasu yankuna na jihar tare da maido da wutar lantarki a gabashin Gujba, wanda ya dade ya lalacewa sakamakon rikicin Boko Haram.
A karkashin gwamnatinsa, sama da al’ummomi 400 ne a fadin shiyyoyin uku suka amfana da ingantaccen hanyoyin shigan kudi tare da samar da ayyukan cigaba da suka hada da tsawaita layukan rarraba 33KV da 11KV da kuma inganta wutar lantarki a wurare daban-daban.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa ta samar da sabon layin watsa wutar lantarki mai karfin 330/132/33 KV tare da tabbatar da samar da wutar lantarki ga jami’ar jihar Yobe da kuma asibitin koyarwa na jihar Yobe.
Wani abin sha’awa shi ne, gwamnatinsa ta samar da taransfoma sama da 100 masu karfin KVA 300 zuwa 500 a muhimman wurare da suka hada da cibiyoyin lafiya da makarantu a jihar, baya ga samar da taransfoma ga wuraren da ake da yawan jama’a domin samar da ingantacciyar wutar lantarki, mai dorewa da kuma daidaito.
Samar da wadannan ci gaba guda biyu zai karfafa tattalin arziki da saukaka rayuwar mutanen karkara da kuma inganta harkokin ilimi, lafiya, kasuwanci ga al’ummar karkara da kauyukan jihar baki daya.
Gwamna Buni yana inganta rayuwar mutanen jihar Yobe ta hanyar samar musu da ingantacciyar hanyar gudanar wa.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.






