

SANARWA.
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
16 days ago
Shugaban karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya karyata/barranta Kansa ga labarai da rubuce-rubucen da ke yawo a garin Potiskum dake nuni da cewa zai tsaya takarar gwamna a zaben 2027 mai zuwa.
Karamar Hukumar Potiskum, Shugabanta, da Gwamnatin Jihar Yobe ba su da masaniyar wannan batu.
Da fatan za a yi la'akari da labarin a matsayin labari maras tushe, ƙirƙirarre, kuma mara amfani.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.




