


SANARWA
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
8 days ago
Sanarwa daga Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukumar Potiskum
Shugaban Ƙaramar Hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya karyata jita-jitar cewa yana goyon bayan wani ɗan takara a zaben Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke tafe.
Ya ce wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma gwamnatinsa ba ta da hannu a harkokin cikin gida na ƙungiyar.
“Babu wani ɗan takara da nake mara wa baya. Abin da na fi mayar da hankali akai shi ne kyakkyawan shugabanci, zaman lafiya, da ci gaban Potiskum gaba ɗaya,” in ji shi.
Ya kuma jaddada cewa zai ci gaba da zama mai adalci ga duk ƙungiyoyi, tare da samar da yanayin da kowa zai ci gajiya nan gaba.
Mal. Ibrahim M. Nura
SA Information & Communication
Ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Potiskum.



3 days ago

20 hours ago