



Sakon Godiya Da Bangajiya;
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
25 days ago
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Ina mai fara wa da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, kamar yadda Ya ce: “Idan kuka yi godiya, lalle Zan ƙara muku.” (Suratul Ibrahim: 7).
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad ﷺ wanda ya ce: “Wanda bai gode wa mutane ba, bai gode wa Allah ba.” (Tirmizi).
Ina mai miƙa sahihin sakon godiya da ban gajiya ga iyaye, ‘yan uwa, abokai da dukkan masoya da suka halarci daurin aurena da aka daura a ranar Juma’a, 2 ga Janairu, 2026.
Kasancewarku tare da ni a wannan rana mai albarka abin alfahari ne da ni’ima babba daga Allah.
Ga waɗanda Allah bai ba su ikon halarta ba, ina godiya ta musamman bisa addu’o’i da kyawawan fatan alheri.
Ba ni da abin da zan saka muku face addu’a da Fatan Alkairi, ina roƙon Allah Ya saka muku da alheri, haka kuma, ina neman afuwa ga duk wanda muka yi wa ba daidai ba, da sani ko ba da sani ba. Allah Ya gafarta mana gaba ɗaya, Ya albarkaci aurena, Ya kuma ɗora zumunci da ƙauna a tsakaninmu.
Allah Ya saka da alheri, Ya haɗa zukatanmu kan alkhairi.
Mal. Ibrahim M. Nura
SA Information and Communication
Office of the Executive Chairman Potiskum LGA.
13 days ago