Sabuwar Potiskum: A Bangaren Kasuwanci, Noma, Da Masana'antu bayan Gwamna Buni Ya Tabbatar Da Alkawarin sa
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Sabuwar Potiskum: A Bangaren Kasuwanci, Noma, Da Masana'antu bayan Gwamna Buni Ya Tabbatar Da Alkawarin sa

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

12 hours ago

... Karamar Hukumar Potiskum na ci gaba da daukar ajandar cigaba a matsayin cibiyar kasuwanci ta jihar Yobe.
.
.
Sabon fuskar Karamar Hukumar Potiskum a daidai lokacin da Gwamna Buni ya tabbatar da alkawuran yakin neman zabensa da kuma tabbatar da matsayin karamar hukumar a matsayin cibiyar kasuwanci da noma ta jihar Yobe.

Kokarin da gwamna Buni ya yi na karfafa harkokin kasuwanci a karamar hukumar domin samun tsarin kasuwanci wanda zai samar da tsarin gasar kasuwanci mai kyau da kuma inganta darajar kasuwanni da masana’antu a karamar hukumar Potiskum sun hada da.

1. Samar da Kasuwar Zamani mai inganci (Potiskum Modern Market) mai tsarin kasuwannin duniya wanda zai yi tasiri matuka wajen bunkasar tattalin arziki da daidaita harkokin kudi, da samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar ‘yan kasuwa a karamar hukumar Potiskum.

2. Samar da katafaren tashan tirela (trailer park) wanda zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki da bunkasar sufuri, kuma yana dauke da fasahar zamani da ta sa ya zama mafi girma a Afirka.

Kasancewar karamar hukumar Potiskum tana da tasiri a bangaren manyan motocin dakon kaya (trailers) samar da katafaren tashan manyan motocin zai inganta tattalin arziki da samar da kudin shiga ga al’ummar karamar hukumar Potiskum da jihar Yobe baki daya.

3. Garage na kanikanci kuma na zamani mai ingancin samar da ayyukan yi, inganta sana’ar injuna, da tabbatar da walwalar mazauna karamar hukumar Potiskum, samar wa al’ummar jihar tsarin sufuri mai inganci, da kara hanyoyin samun kudin shiga, da kyautata jin dadin al’umma.

4. Kamfanin sarrafa rid'i, wanda kuma zai samar da ingantaccen tsarin ciniki bisa tsarin zamani na tantancewa da tace rid'in da ake da shi a cikin gida, manufa ce da za ta kawo sauye-sauye a fannin hada-hadar kasuwanci da zai yi tasiri wajen baiwa masu zuba jari cikakkiyar dama da kwanciyar hankali wajen kulla huldar kasuwanci da karamar hukumar Potiskum da jihar Yobe baki daya.

5. Makarantun sikandare na model, mega, da na jeka-ka-dawo na ‘yan mata wadanda aka samar da tsarin tafiyar wa na zamani tare da cikakkun kayan aiki da zasu taimaka wajen inganta ilimi da zamanantar da shi.

Haka kuma tsarin ya kawar da gibin da ya taimaka wajen dakile ilimin ‘ya’ya mata a karamar hukumar, wanda a yanzu ya ba ‘ya’ya mata cikakken damar karatu a gidajen iyayensu a sabbin makarantun da Gwamna Buni ya kafa.

Gwamna Buni ya taka rawar gani wajen tabbatar da jin dadin al’ummar karamar hukumar Potiskum da kuma tattara bayanan sirri domin bunkasa harkokin gudanarwar karamar hukumar Potiskum.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

438
6570
12 hours ago

Madson Laylah King Niklaus Ross Alena Wilds Anna Ramirez Jayce Gonzales Paris Jepson Mariam Gilmartin Gianna Pooler Hayden Bumpus Cedric Roberts Kiaan Ramirez Declan Fifer Hailey Mcelrath Arjun Watson Carl Myhre Dylan Cheshire Ander Sanchez Kannon Wood Curtis Baker Damien Peay Kyree Pettiford Emanuel Rivera Gideon Haga Braylon Ping Louise Alvarez Melvin Killeen Rohan Covell Guadalupe

Sign in to post a comment.


Sign In