Sabuwar ma'aikatan kula da dabbobi (Ministry of livestock Development) a jihar Yobe da Gwamna Buni ya kirkira zai taimaka gurin bunkasa tattalin arziki da Samar da ayyukan yi.
ibrahim muhammad nura
Image
Image

Sabuwar ma'aikatan kula da dabbobi (Ministry of livestock Development) a jihar Yobe da Gwamna Buni ya kirkira zai taimaka gurin bunkasa tattalin arziki da Samar da ayyukan yi.

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

4 days ago

Mal. Ibrahim M Nura
Executive Director,
Yobe State Youth Concern For Good Leadership.

Kasancewar Ma'aikatan kula da dabbobi (Ministry of livestock Development) Yana taka mihimmiyar rawa wajen inganta cigaba me dorewa a fannin kiwon dabbobi, Wanda hakan na iya tasiri matuka gurin habaka tattalin arziki jiha ko kasa, na yaba wa gwamna Buni bisa kirkirowa ko samar da wannan ma'aikatan mallakin jihar Yobe.

Bayan Samar da ayyukan yi ga dubban matasa da rage zaman banza a tsakanin al'ummar jihar mu wannan sabon ma'aikatan zai taimaka ta wadannan bangarorin.

1. Ma'aikatan za ta iya yin aiki don inganta ayyukan kiwon dabbobi, inganta lafiyar dabbobi, da kuma karfafa hanyoyin kiwo masu inganci. Kiyaye tsarin kiwon bisa tafarkin zamani na iya samar da kyakkyawan tsarin da za'a iya sayar da dabbobin har a kasuwannin ketare, Wanda hakan zai Kara kawo kudin shiga ga jihar da su kansu masu kiwon dabbobin domin tsarin zai baiwa baki damar shigowa yin cinikayya da makiyayan mu.

2. Bangaren zai Samar da ayyukan yi ga dumbin jama'a da suka hada da fadada harkar manoma, makiyaya, likitocin dabbobi, da sauran fannonin kwarewa a bangaren noma da kiwo. Ta hanyar cigaban tattalin arziki Kai tsaye ma'aikatan za ta iya taimakawa wajen samar da sabbin ayyukan yi da karfafa ayyukan tattalin arziki har izuwa yankunan karkara.

3. Ma'aikatan kula da dabbobin zai taimaka gurin bunkasa wa, saukaka wa, tare da zamanan tar da hanyoyin fitar da kayayyakin kiwo kamar Nama, kaho da fatan dabbobi, hakan kuma zai taimaka matuka gurin Samar da kudaden shiga da inganta daidaiton ciniki a ciki da wajen kasuwannin jihar sannan ya kawo bunkasa da hada hadan kudaden waje cikin tattalin arzikin jihar.

4. Zai karfafa daraja da kima wa bangaren kamar sarrafa Nama, kiwo, kaho da fata na iya Kara daraja ta hanyar Samar da samfuran zamani da Karin hanyoyin samun kudin shiga, ma'aikatan na iya taimaka wa makiyaya ta hanyar samar da dabbobi masu kyau da tsari bisa tsarin shirye-shiryen tallafawa ta hanyar karfafa wa makiyayan.

5. Ma'aikatan zai taimaka gurin jawo hankalin gwamnati da 'yan kasuwan duniya gurin zuba jari a bangarorin noma da kiwo, domin bincike da habaka fannin kiwo da noma na iya samar wa da kirkirar, aikin yi, da kuma wadatattun aiki da tsarin gudanar wa na zamani. Wato ma'aikatan nan zai iya tallafawa Shirye shiryen binciken da aka mayar kan inganta kiwon dabbobi na duniya kamar rigakafin cututtuka da ayyukan noma masu dorewa.

6. Sannan ma'aikatan zai taimaka gurin aiwatar da ka'idoji da suka shafi samar da dabbobi, amincin abinci, da jindadin dabbobi Wanda hakan zai taimaka gurin bunkasa kiwon lafiya da karfafa amana tsakanin mabukatan samfuran dabbobi daga ko ina a fadin duniya, wannan amanar kuma zaiyi tasiri akan tsarin sanya hanun jari da tallafawa harkokin noma da kiwo don Samar da cigaba me dorewa.

7. Samuwar ma'aikatan Livestock Development din zai sake taimakawa gurin inganta ababen more rayuwa kamar hanyoyin zirga-zirga, wuraren yanka, wuraren ajiyar sanyi, da hada-hadar kasuwa, kuma hakan na iya taimakawa wajen saukaka zirga-zirgar dabbobi da kuma rage asarar da ke afkuwa sakamakon rikicin manoma a fadin jihar yobe.

8. Ma'aikatan Livestock Development din zai kuma taimaka gurin Samar da shirye shiryen horarwa, ayyukan habaka harkar noma da kiwo, da Karin albarkatun kudi ga manoma da makiyaya dabbobi a fadin jihar, inda na iya habaka kwarewar su da habaka ayyukan yin su. Hakan kuma zai iya samar da ingantacciyar kudin shiga ga manoma da cigaban sassan gaba daya.

Da wannan nake ganin cewa Gwamna Buni ya cancanci yabo da jinjina gurin kawo tsarin da zai bunkasa tattalin arzikin mu bayan tsare tsaren sa na inganta kasuwannin jihar da farfado da masana'antu.

Domin ta wannan hanyar kadai idan aka maida hankali kan fannonin duka, kiwon dabbobin zai taka mihimmiyar rawa wajen habaka tattalin arziki a fannin kiwon lafiya da bunkasa tattalin arzikin jihar Yobe Baki daya.

66
994
4 days ago

Sign in to post a comment.


Sign In