




Mun kafa cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 140, mun inganta guda uku zuwa manyan asibitoci
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
16 days ago
- Gwamna Mai Mala Buni ya shaida wa wakilan Blueprint Newspaper.
Gwamnan jihar Yobe H.E Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ya shaida wa wakilan jaridar Blueprint Newspaper cewa gwamnatin sa ta samar da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 140, tare da inganta guda uku zuwa manyan asibitoci da kuma inganta manyan asibitoci guda hudu zuwa asibitin kwararru.
Gwamnan ya shaida musu ne a yayin da suka kai masa Ziyara Na musamman domin karramashi a matsayin gwarzo gwamnan da yafi kowani Gwamna tasiri a Bangaren kiwon lafiya na shekarar 2025 bisa nasarorin da kiwon lafiya ya Samu a jihar karkashin gwamnatin sa.
Gwamnan ya Kuma yaba wa jaridar Blueprint Newspaper din bisa yadda ta amince tare da nuna gamsuwa da nasarori da tsare-tsaren da gwamnatinsa ta kaddamar a Bangaren kiwon lafiya a fadin jihar Yobe.
"Nayi farin ciki da ku da kanku kuka samu gamsuwa da tsare-tsaren mu na inganta lafiya, Kuma abinda Kuka Gani da idon ku a jihar mu ya baku shaida na zahiri Akan irin yanda muke cigaba da hobbasa wa don karfafa kiwon lafiya." Inji Shi
Gwamnan ya kuma jaddada irin kwazon gwamnatin sa da irin nasarorin da take samu a Bangaren kiwon lafiyan.
"Mun Samar da ingantattun cibiyoyin kiwon Lafiya matakin farko guda 140, Mun inganta cibiyoyin kiwon Lafiya guda uku zuwa manyan asibitoci, sannan mun sauya manyan asibitoci guda hudu zuwa asibitin kwararru, Mun Kuma gyara asibitin koyar wa da samar da na'urorin zamani sannan muka kafa cibiyar kula da mata da jarirai mafi tasiri da girma a najeriya duk a yunkurin mu na kawo ingantaccen hanyar kula da lafiyar Jama'a." Gwamna Buni ya cigaba da fada.
Gwamnan ya Kuma sadaukar da lambar yabon da karramawar ga illahirin al'ummar jihar Yobe da suka nuna yardar su suka bashi damar cigaba da jagorantar su.
Mal. Ibrahim M Nura
Special Assistant on Information and Communication to the executive chairman of Potiskum local government area.








































11 days ago