Hon. Salisu Muktari yayi nasarar dawo da Gonaki (Orchard) wa Potiskum LGA bayan shafe shekaru shida ana Shari'a
ibrahim muhammad nura
Image

Hon. Salisu Muktari yayi nasarar dawo da Gonaki (Orchard) wa Potiskum LGA bayan shafe shekaru shida ana Shari'a

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

13 hours ago

... Chairman din yana cigaba da tabbatar da aniyar sa na kwato kadarorin gwamnati da wasu sukayi Ruf da ciki akai.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari yayi nasara kan Shari'ar Gona/Fili mallakin karamar hukumar Potiskum Bayan kwashe shekaru shida ana gwabza Shari'a tsakanin karamar hukumar da Wani me Suna Alh. Musa Dan Dutse.

A ranar juma'a ne 27th, ga Watan Yuni 2025 kotun daukaka kara Bayan sauraron hujjoji daga bangarorin guda biyu ta yanke hukunci tare da mallaka wa karamar Hukumar Potiskum Gona/Filin noma da ke kusa da Gadan Kano Akan hanyar Kano Bayan tabbatar da cewa mallakin karamar hukumar Potiskum din ne.

Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum din ya bibiyi lamarin ne domin kwato kadarorin gwamnati da aka bayar da su ba bisa ka'ida ba, sannan ya nuna kwazo da jajircewa gurin bin hanyoyin da suka dace domin kwato duk wani kadarar gwamnatin da ke hannun mutane domin cigaban al'ummar Potiskum.

Gonan/Filin zai taimaka matuka gurin habaka tattalin arzikin Karamar Hukumar, ta inda sashen noma na Karamar hukumar zasu iya amfani dashi ta hanyoyi da daban-daban wajen karfafa tattalin arziki da walwala a bangaren da kuma Karamar Hukumar Potiskum din.

Chairman din dai yayi alwashin hana Duk wani nau'in cin hanci da rashawa da kuma bin diddigin duk wata kadarar gwamnatin da aka mallaka wa wasu ba bisa ka'ida ba don dawo wa da karamar hukumar kadarar ta.

Hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke Bayan shafe shekaru shida ana Shari'a sun tabbatar da cewa karamar Hukumar Potiskum ce ke da alhakin mallakar gonakin (orchard) da ke kusa da Gadan Kano Kan hanyar kano a karamar hukumar Potiskum.

Hon. Salisu Muktari ya nuna jajircewar sa kan tabbatar da gaskiya ta hanyar bin diddigin Shari'ar don kwato kadarorin karamar hukumar Potiskum.

Gaskiya Maganin Karya.

Mal. Ibrahim M Nura
Mataimaki na Musamman Akan watsa labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

148
2220
13 hours ago

Gilmartin Gianna Cruz Gatlin Enlow Eugene Million Rory Anderson Ellen Castillo Nixon Murphy Abigail Stewart Halle Fedor Deandre Ramirez Jayce Edelstein Journey

Sign in to post a comment.


Sign In