

Hon. Salisu Muktari Yayi Kira Ga Al’ummar Karamar Hukumar Potiskum, ‘Yan Kasuwa, Ma’aikatan Gwamnati, Da Matasa Da Su Sabunta Ko Rijistar Sabon Katin Zabe
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
7 days ago
... Kiran ya biyo bayan hada-hadar masu ruwa da tsaki na "ci gaba da rijistar masu kada kuri'a" a karamar hukumar Potiskum.
•
•
Shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari, ya yi kira ga al’ummar karamar hukumar Potiskum, ’yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, da matasa da su sabunta ko yin rijistar sabbin katunan zabe.
Shugaban ya kuma bayar da tabbacin cewa dole ne a mai da hankali wajen wayar da kan al’umma kan ka’idojin rajista, ya kuma yi kira ga wadanda suka kai shekarun yin rajista da su fito su yi rajistar sabbin katin zabe, domin ita ce kadai hanyar da za ta iya baka damar kada kuri’unka bisa doka.
“Yayin da muke ci gaba da daukar sabbin masu kada kuri’a wadanda suka cika sharuddan zabe a duk kakan zabe na shekara 4 da akeyi a kasarnan, ya zama wajibi mu kuma mayar da hankali wajen ganin al’ummarmu da suka kai shekarun yin rajistar zabe sun zo sun yi rajistar katin zabe domin samun damar shiga cikin layukan zabe don kada kuri’u a ranakun zabe.
“Kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa bayan taron tattaunawan kwamitin “Ci gaba da Rijistar Zabe Na Kasa” a fadin kasar nan da aka gudanar a yau, 23 ga watan Agusta, 2025 a karamar hukumar Potiskum, an sanar da fara rajistar sabon katin zabe a karkashin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kuma an fara gudanar da aiki shafin yanar gizon tun ranar 18 ga watan Agustan 2025.
“Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa za a fara rijistar da kai tsaye a ranar 25 ga watan Agusta, 2025, a ofisoshin INEC na jihohi talatin da bakwai (37) da kuma kananan hukumomi 774 a fadin Najeriya, don haka muke kira ga jama’ar mu da su himmatu wajen rajista da karbar katin zabe, domin ita ce kadai hanyar da za a baiwa kowa damar kada kuri’arsa." Inji Hon. Salisu Muktari
Shugaban ya kuma yi kira ga karamar hukumar Potiskum a matsayin karamar hukuma mai yawan jama’a inda ya bukace su da su yi amfani da tsari wajen yin rijistar domin al’ummar mu su amfana.
“A matsayinmu na karamar hukumar da ke da yawan al’umma a cikin kananan hukumomi 17 na jihar Yobe, yana da kyau mu mayar da hankali wajen karbar katin zabe domin ita ce kadai al’ummarmu za su amfana domin ita kanta yawan al’ummar arziki ne." Ya kara da cewa,
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.






