Hon. Salisu Muktari ya ziyarci kasuwan waya na Potiskum, ya jajanta musu bisa yadda jami’an tsaro suka muzguna musu
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Hon. Salisu Muktari ya ziyarci kasuwan waya na Potiskum, ya jajanta musu bisa yadda jami’an tsaro suka muzguna musu

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

11 days ago

...Ya ba su tabbacin bin kadunsu tare da ba da tabbacin za a ba su taimako domin rage radadin asarar da suke ciki.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari ya ziyarci kasuwan waya na Potiskum (PPC) domin jajanta musu kan musgunawa da jami’an tsaro suka yi musu a jiya lahadi 9, 2nd, 2025, da yamma.

Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa suna bin diddigin al'amarin don bin hakkin duk Wanda aka zalunta kuma ya ce yunkurin cin zarafi ne da jihar da karamar hukumar Potiskum ba za su lamunta ba.

“Wannan lamari da ya faru a kasuwar ya saba wa doka kuma babu wani dalili ko doka da za ta ba jami’an tsaro damar shiga kowani irin kasuwane domin aiwatar da wannan danyen aikin.

“Ina nuna alhinina ga asarar dukiya tare da isar da sakon jajen gwamna kan wannan mummunan lamari da ya samu ‘yan kasuwarmu na Potiskum." Hon. Salisu Muktari Said

Shugaban ya kara da cewa gwamnatin jihar Yobe za ta samar wa ‘yan kasuwar wurin da za su rika gudanar da sana’arsu ba tare da wata fargaba ba.

“A matsayina na shugaban karamar hukumar Potiskum, zan samar da wani katafaren fili inda za a gina kasuwar tafi da gidanka na zamani mai inganci ga ‘yan kasuwarmu na waya a karamar hukumar Potiskum.

“Ina mai tabbatar muku da cewa zan ci gaba da tabbatar da cewa tare da bibiya don gwamnatin jiha ta gina wani gini na zamani a wannan fili da zan samar muku, zaman lafiyarmu da zaman lafiyar al’ummar karamar hukumar mu ya ta’allaka ne a kan tsarin gudanar da mulki nagari da kuke da shi a kasuwannin ku, don haka muna tare da ku, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don kare martabar ku." Hon. Salisu Muktari ya kara da cewa

Mal. Ibrahim Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

225
3381
11 days ago

Sign in to post a comment.


Sign In