Hon. Salisu Muktari Ya Yabawa Sen. Ibrahim Mohammad Bomai Bisa Tallafawa Marasa karfi da gajiyayyu 2,000 Da Abinci da kudi
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
6 days ago
•
•
Yace wannan gagarumin kokari yazo a daidai lokacin da al'umma ke cikin tsananin bukata.
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya yabawa Sen. Ibrahim Mohammad Bomai bisa tallafawa nakasassu da marasa galihu da kayan abinci da abubuwan da ba na abinci ba a fadin kananan hukumomi 4 na shiyyar B.
Shugaban ya tabbatar da cewa wannan shiri zai taimaka matuka wajen rage wahalhalu da fatara ga al’ummar yankin musamman nakasassu da marasa karfi, domin su ne suke da bukata ta musamman.
Sanata Ibrahim Mohammad Bomai ya tallafa wa nakasassu da marasa galihu da buhunan shinkafa har 2000 tare da kyautar kudi domin saukaka harkokin gudanarwa.
Shugaban zartarwar Hon. Salisu Muktar ya ce:
“Abin da jama’a ke bukata a yanzu shi ne kyakkyawan wakilci domin idan aka samu wakilci nagari ne kawai mutane za su ga daidai sannan su samu ribar dimokuradiyya kai tsaye daga wakilansu.
“Idan muka mukayi la'akari da baya, mutanen kudancin jihar Yobe sun samu wakilci nagari a karkashin Sanata Ibrahim Mohammad Bomai.
“An ceto yankinmu ta hanyoyi da dama, mun samu dakunan karatu na zamani da yawa a kudancin jihar Yobe a karkashinsa, mun samu makarantu da asibitoci da za su taimaka mana matuka wajen gina rayuwarmu.
Ya kuma ce bayar da tallafi kai tsaye ga al’ummar kudancin jihar Yobe wani sabon abu ne da jama’a ke kallo a matsayin tsarin da zai taimaka matuka wajen ci gaba da inganta al’umma.
“Tabbas bayar da tallafin kai tsaye da Sen. Ibrahim Mohammad Bomai yayi zai taimaka wajen inganta al’umma da kuma rage radadin talauci da al’ummarmu ke fama da shi a sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kasar nan ke fama da su baki daya.
"Muna mika godiyarmu ga Sanatan nan bisa jajircewarsa na samar da ayyukan raya kasa da kuma bunkasa yankin mu cikin shekaru 6 da ya shafe yana wakiltar mu a majalisar dattawan Najeriya." Hon. Salisu Muktari ya sake tabbatar wa
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.