Hon. Salisu Muktari Ya Tallafawa Ma'aikatan Karamar Hukumar Potiskum, Marubuta Social Media Na APC Da Kudi Da Kayayyakin Bukatu
ibrahim muhammad nura
Image

Hon. Salisu Muktari Ya Tallafawa Ma'aikatan Karamar Hukumar Potiskum, Marubuta Social Media Na APC Da Kudi Da Kayayyakin Bukatu

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

3 days ago

... Ya umurci cewa a baiwa kananan ma'aikata, P.A.s, leburori, direbobi, da shugabannin sashe, fifiko.
.
.
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya tallafawa ma’aikatan karamar hukumar Potiskum da marubutan kafafen yada labarai na jam’iyyar APC na Potiskum da kudi da kayan masarufi.

Shugaban ya bayar da tallafin ne ga ma’aikatan kananan hukumomin domin inganta jin dadin su a yayin bukukuwan karamar Sallah da ake shirye-shiryen yi a ranar Juma’a 6 ga watan Yuni, 2025.

Haka kuma ya bayar da tallafin kudi ga marubutan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na karamar hukumar Potiskum don inganta ayyukansu da kuma ci gaba da samar musu da matsuguni a cikin jam’iyyar tare da kula da jin dadinsu don gudanar da ayyukan jam’iyyar da kuma gudanar da bukukuwan karamar Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban kungiyar ma'aikatan karamar hukumar Potiskum (Nulge Chairman) Danbaba Ali ya ce:

"Tabbas shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari, ya jajirce wajen tabbatar da jin dadin ma’aikatanmu ta hanyar kula da mu a lokutan bukukuwan addini da sauran abubuwan da ke bukatar taimakon kudi, kuma muna daukar hakan a matsayin kyakkyawar alaka da kyautata mu'amala ga ma’aikatanmu.

“Mun sayi buhunan shinkafa mai tsafta 100Kg, kuma mun raba su ga rukunin ma’aikatu 7 na karamar hukumar Potiskum, kuma bisa umarninsa, ya jaddada ba da fifiko ga masu kananun karfi da kananan ma’aikatan karamar hukumar." Inji shi

Sassan da suka ci gajiyar tallafin kai tsaye sun hada da Sashen Admin, Sashen Aikin Noma, Sashen Kasafi da Tsare-tsare, Sashen PHC, Sashen Ayyuka, da LEA.

Ya kuma tallafa wa wasu daga cikin marubutan jam’iyyar APC na karamar hukumar Potiskum da kudi, 50,000 da 25,000, domin gudanar da bukukuwan Sallah.

Wannan karimcin ya nuna alheri da damuwa ga jin dadin ma'aikatan karamar hukumar da masu yiwa jam'iyyar APC hidima a kafafen sada zumunta da kuma niyyar tabbatar da manufofin mai girma Gwamna Hon. Mai Mala Buni FCIA CON COMN domin inganta rayuwar ma'aikata da kuma al'ummar jihar Yobe baki daya.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

6
3 days ago

Sign in to post a comment.


Sign In