




Hon. Salisu Muktari ya samar da boreholes masu amfani da hasken rana a Garin Abba, Mazagane, da Tiken Shanu na karamar hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
17 days ago
.... Inganta rayuwar al'ummar karamar hukumar Potiskum na daya daga cikin manyan manufofin Hon. Salisu Muktari.
•
•
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya samar da boreholes masu amfani da hasken rana a garuruwan Garin Abba, Mazagane, da Tiken Shanu domin saukaka wa al’umma hanyoyin samun ruwan sha don amfanin yau da kullum.
Ganin yadda al’ummar garin da kewaye ke fuskantar kalubalen karancin wutar lantarki wanda ya sa jama’a suka shiga cikin wani mawuyacin hali na rashin ruwa, shugaban karamar hukumar ya dauki matakin sauya lamarin tare da kafa boreholes masu amfani da hasken rana domin saukaka wa al’ummar karamar hukumar Potiskum.
Shugaban ya samar da boreholes masu amfani da hasken rana da dama a fadin karamar hukumar tun daga garin har zuwa kauyukan da ke wajen garin domin inganta rayuwarsu da saukaka musu hanyoyin samun ruwan sha domin amfanin yau da kullum.
A yayin ziyarar gani da ido a garin Mazagane, daya daga cikin wadanda suka amfana da boreholes masu amfani da hasken rana a garin, Mal. Auwalu Mazagane ya tabbatar da cewa;
“Shekara guda da ta wuce, a cikin watan Ramadan muna fuskantar matsalar karancin ruwa, sai mun yi tafiya mai nisa don samun ruwan da za mu iya amfani da shi da kuma sha a lokacin bude baki.
“Wani lokaci muna iya sayen jarkar ruwa mai lita 25 a kan Naira 1000 domin dolene sai mun biya bukatun kanmu, amma bayan samar da wadannan boreholes da shugaban gudanarwar mu ya yi, wanda ke da kishinmu da al’ummarmu, yanzu muna cin moriyar ruwa kyauta ba tare da kashe ko kwabo ba.
“Muna matukar farin ciki da abin da shugaban karamar hukumarmu Hon. Salisu Muktari ya yi mana, kuma a madadina da daukacin al’ummar Mazagane muna mika godiyarmu a gare shi da duk masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Potiskum" Cewar Mal. Auwalu Mazagane
Shugaban ya samar da boreholes a yankuna da dama na karamar hukumar Potiskum; za mu ci gaba da kawo sauye-sauyen da aka samu a kowane yanki tare da hotuna masu nuna cikakkun bayanai.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da hulda da jama'a ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.