Hon. Salisu Muktari ya sake samar da ingantaccen Sienna XLE ga ma’aikatan karamar hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image

Hon. Salisu Muktari ya sake samar da ingantaccen Sienna XLE ga ma’aikatan karamar hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

6 days ago

...Shugaban yana samar da motoci masu ingancin ne don inganta ayyukan ma'aikatan Karamar hukumar.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya sake samar da ingantaccen Sienna XLE ga ma’aikatan karamar hukumar Potiskum.

Shugaban ya samar da wadannan motocin ne a kokarinsa na inganta ayyukan ma’aikatan karamar hukumar da samar musu saukin zirga-zirga yayin gudanar da ayyukansu na yi wa al’umma hidima.

A satin da ya gabata ne shugaban karamar hukumar ya gyara tare da samar da motoci kirar Peugeot 406 guda biyu, a manufar sa na samar da saukin sufuri ga ma’aikatan karamar hukumar domin gudanar da ayyukansu a fadin karamar hukumar.

Shugaban zartarwa na karamar hukumar yayi alwashin karfafa gwiwar ma’aikatan karamar hukumar ne a kokarinsa na tabbatar da aniyar mai girma gwamnan jihar Yobe H.E. Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, na tabbatar da cewa an samar da ayyuka masu kyau da inganci a dukkan fannoni.

“Ma’aikatanmu sune kashin bayan nasararmu, kuma muna da tsare-tsare na inganta rayuwarsu, domin yawancin ma’aikatanmu sun fito ne daga wasu kananan hukumomin jihar Yobe.

"Samar musu da motoci masu kyau da inganci don saukaka tafiyarsu abu ne mai matukar amfani a gare mu baki daya." cewar Hon. Salisu Muktari

Shugaban ya himmatu wajen inganta rayuwar al’umma tare da samar musu da saukin aiwatarwa a kowane fanni.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

15
231
6 days ago

Hall Nicole

Sign in to post a comment.


Sign In