




Hon. Salisu Muktari Ya Mayar Da Ofishin Vigilante Zuwa Tsohuwar Sakatariyar Potiskum LGA
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
18 days ago
...Bayan Farfado da Tsohuwar Sakatariyar 'Yan Vigilante Sun Samu Hedikwata a ciki.
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari ya samar da hedikwata ga jami’an ‘yan banga a tsohuwar sakatariyar karamar hukumar Potiskum biyo bayan farfado da sakatariyar da ya yi bayan an yi watsi da ita tsawon shekaru.
Samar musu da ofishin zai kara musu kwarin guiwa wajen taimaka wa don karfafa tsaron al’umma da dukiyoyinsu a karamar hukumar potiskum.
Babban jami’i a rukunin DC Sani Muhammad Kani ya ce. “Muna samun goyon baya da yawa daga shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari don inganta tsaro a karamar hukumar Potiskum.”
Ya kuma tabbatar da cewa: “Da farko mun bukaci karamar hukumar Potikum da ta samar mana da ofishi domin karfafa kokarinmu na dakile matsalar tsaro a karamar hukumar, in da shugaban karamar hukumar ya ba mu mafaka a sakatariyar karamar hukumar.
“Bayan zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, an kona tare da yi mana sace sace a ofishin da ya bamu a sabuwar sakateriyar, Wanda bayan nan kuma muka sake mika kokenmu ga shugaban karamar hukumar domin ya samar mana da mafita domin mu samu mafita ga bukatar mu na ofis don ci gaba da aikinmu.
“Shugaban karamar hukumar bai gajiya na ya gyara mana wani bangare na tsohuwar sakatariyar na, inda a yanzu muna da Dibision namu da Area Command a karkashin wannan tsohuwar sakatariyar da ya farfado da ita, don haka ba mu da wani kalma da za mu yi amfani da shi wajen godiya ga shugaban karamar hukumar mu mai albarka Hon. Salisu Muktari." DC Mohammed Kani ya kara da cewa
Hoton da ke ƙasa yana dauke da yadda ofishin yake a cikin tsari da tsari na zamani bayan mallakar wan da shugaban karamar hukumar yayi musu.
Mal. Ibrahim Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.