Hon. Salisu Muktari Ya Maida Sansanin Sojoji Zuwa Lailai, Ya Gyara Ofishin Mopol Dake Titin zuwa Damaturu A Karamar Hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image

Hon. Salisu Muktari Ya Maida Sansanin Sojoji Zuwa Lailai, Ya Gyara Ofishin Mopol Dake Titin zuwa Damaturu A Karamar Hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

14 days ago

... Samar da matsuguni mai kyau da kuma inganta wuraren aikin jami'an tsaron zai karfafa tsaro a karamar hukumar.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya mayar da sansanin jami’an tsaron soji daga unguwar Rest-house zuwa anguwar Lailai tare da gyara da sabunta sashen Mopol dake kan titin Damaturu a karamar hukumar Potiskum.

Shugaban karamar hukumar ya yi haka ne domin karfafawa jami’an tsaro gwiwa tare da samar musu wurin gudanar da dukkan ayyukansu cikin kwanciyar hankali da lumana don tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu a karamar hukumar Potiskum.

Jami’an tsaron sun yi sansani ne a anguwar Rest-house da ke kan titin Kano, a karamar hukumar Potiskum, sunyi sansanin ne sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi karamar hukumar a shekarun baya, shugaban karamar hukumar ya dauki matakin mayar da su Lailai domin ya kara musu kwarin guiwa da kawar da su daga cikin al’umma zuwa sansanin zamani.

A sabon sansanin da ya samar musu a anguwar Lailai ya samar musu da tsarin ruwa mai kyau da rijiyoyin burtsatse na zamani masu amfani da hasken rana da ingantaccen wutar lantarki wanda zai taimaka musu matuka wajen samar da tsaro ga al’umma a karamar hukumar.

Shi kuwa sashin Mopol, shugaban karamar hukumar ya gyara ta tare da sabunta ta sannan ya yi mata katanga da rijiyoyin burtsatse na zamani da wutar lantarki.

An dade da yin watsi da Ofishin Mopol din, amma Hon. Salisu Muktari ya waiwaye su inda ya sabunta rukunin domin karfafa gwiwar jami’an tsaro wajen samar da ingantaccen tsaro ga al’umma.

Samar da tsaro da ingantaccen tsarin kiwon lafiya na daga cikin manyan abubuwan da Hon. Salisu Muktari yake baiwa fifiko a gwamnatinsa.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

15
238
14 days ago

Sign in to post a comment.


Sign In