




Hon. Salisu Muktari ya karbi bakoncin tawagar gwamnatin jihar Yobe, da shuwagabannin kasuwan waya na Potiskum sakamakon iftila'in da ya samu su
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
11 days ago
... Ya yaba da kokarin mai girma Gwamna H.E Hon. Mai Mala Buni CON, COMN, na shiga tsakani cikin gaggawa.
•
•
Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin jihar Yobe da tawagar shuwagabannin wasun waya na karamar hukumar Potiskum (PPC).
A lokacin da yake maraba da tawagar gwamnatin, ya mika kokensa, ya kuma yi alkawarin cewa a matsayinsa na shugaban karamar hukumar Potiskum, ba zai yi watsi da irin wannan lamari ba, yana mai yabawa kokarin mai girma gwamna kan yadda ya gaggauta shiga lamarin.
“A matsayina na shugaban karamar hukumar Potiskum, zan yi duk mai yiwuwa don ganin an samar da tsari mai kyau na hana afkuwar irin haka nan gaba.
“Wannan lamarin ya zama tamkar cin mutuncine ga ‘yan kasuwarmu, ba shakka kasuwar waya na karamar hukumar Potiskum wata mafaka ce da ta samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a karamar hukumar Potiskum, kuma dole ne sai an samar da ayyukan yi nagari a tsakanin matasa domin samar da al’umma ta gari mai cike da tsaro da kwanciyar hankali, cin zarafi da cin mutunci da akayi musu a yayin da suke gudanar da kasuwanci barazana ce da ka iya dagula al’umma da kuma kawo cikas ga shirin gwamnati na samar da al’umma ta gari mai cike da zaman lafiya." A cewar Hon. Salisu Muktari
A bangaren tawagar gwamnan karkashin jagorancin mai girma kwamishinan shari'a, Bar. Saleh Samanja ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta bi diddigin lamarin kuma ya yi alkawarin bayar da gudunmuwar naira miliyan goma.
“Mun ji dadin yadda kuke ba gwamnatin jihar Yobe cikakken goyon bayanku, kuma rashin tashe-tashen hankulanku ya tabbatar da cewa kuna kuna so sannan kuna shirye ku samar da zaman lafiya a fadin jihar Yobe da kuma karamar hukumar Potiskum, a madadin mai girma gwamna, muna mika juyayinmu tare da alkawarin bin kadunku a hukumance." Bar. Saleh Samanja ya tabbatar
Mal. Ibrahim Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.