

Hon. Salisu Muktari ya jajirce wajen tabbatar da jin dadin al’ummar karamar hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
4 days ago
... Yana rike da amanar Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, wajen tsarkakewa da kawar da duk wani abu da zai jawo wa al’umma koma baya.
.
.
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya himmatu wajen tabbatar da jin dadin al’ummar karamar hukumar Potiskum ta fuskar inganta ayyukan noma, kiwon lafiya, da lura da ayyukan gwamnati da kadarori.
Shugaban ya tashi tsaye domin tabbatar da nasarar gwamnatin mai girma Gwamna Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Yobe da kuma tabbatar da jin dadin mazauna jihar ta kowane fanni.
Gwamnatin jihar Yobe ta dauki bangaren noma, kiwo, da kiwon lafiya a matsayin bangarorin da suka fi inganci wajen inganta rayuwar al’umma da tabbatar da walwala.
Haka kuma Hon. Salisu Muktari shi ne kan gaba wajen tabbatar da duk wadannan a karamar hukumar Potiskum domin samar da ayyukan da za su daidaita zukatan mazauna karamar hukumar da manufofin gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin amininsa Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN.
Karamar hukumar Potiskum ta na taka rawar gani wajen inganta manufofin gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin mai girma Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, saboda jajircewar Hon. Salisu Muktari na tabbatar da amanar mai girma gwamna wajen kawar da duk wani abu da zai jawo wa al’umma koma baya.
Burin chairman din shi ne a ba da fifiko ga jin dadi da walwalar al’umma.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.






















