Hon. Salisu Muktari Ya Gina Katafaren Ofishi Da babban Fada Ga Hakimin Mamudo A Karamar Hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Hon. Salisu Muktari Ya Gina Katafaren Ofishi Da babban Fada Ga Hakimin Mamudo A Karamar Hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

23 hours ago

...Wannan wani bangare ne na manufofinsa na farfado da martabar sarakunan gargajiya.


Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya gina wa Hakimin Mamudo babban ofishi da fada mai fadi a karamar hukumar Potiskum.

Shugaban ya gyara tsohon tare da gina wa Hakimin Mamudo sabon ofishi da fada a kokarinsa na ingantawa tare da dawo da martabar masarautun gargajiya a karamar hukumar Potiskum.

Hakimin Mamudo dai hakimine na Potiskum ta waje. Hakimin Mamudon ya tabbatar da cewa ya rubuta da takardar neman gyara fadarsa da ke karamar hukumar wa karamar Hukumar, amma hakan bai yiwu ba; A ko da yaushe sai ayi watsi da bukatarsa sai bayan isowar wannan shugaban zartarwa, Hon. Salisu Muktari. Ya samar musu da babban ofishi da fadar zamani.

Hakimin gundumar ya shaida cewar, “Muna samun kulawar shugaban karamar hukumar Potiskum Hon. Salisu Muktari, wanda yake matukar sha’awar karbar korafe-korafen mu tare da neman hadin kan mu wajen tabbatar da tsaro da rayuwar mazauna yankin mu.

"Shekaru da suka gabata na yi ta neman a canza min gidana ko kuma a gyara min gidana, kasancewar ya lalace kuma muna tsoron zama a ciki, amma gwamnatin da ta shude ta yi watsi da mu, yanzu ka ga Hon. Salisu Muktari ya gyara gidan ya zama babban fada mai girma na zamani, don haka tsakaninmu da mai girma shugaban karamar hukumar babu komai sai addu'a." Inji Hakimin Mamudo.

Inganta masarautun gargajiya da kyautata alaka da su na daga cikin kudirinsa na inganta wa da tabbatar da aniyar mai girma gwamnan jihar Yobe H.E. Hon. (Dr.) Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, domin tabbatar da tsaro da walwala ga mazauna jihar Yobe.

Shugaban karamar hukumar Potiskum din ya jajirce wajen kawo kyakkyawan tsari da tasiri a rayuwar al’ummar karamar hukumar Potiskum.

Hotunan da aka makala a kasa sun nuna yadda ofishin da fadar suka dawo bayan da shugaban ya gyara su da kuma sake gina su.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

310
4651
23 hours ago

Mcclean Whitley Chavez Kailey Hughes Royal Cruz Paola Collins Lennon Martinez Kellan Spahr Kellen Murphy Colin Reed Leon Hall Nicole Ping Kinslee Walker Eliel Gilmartin Brynlee Million Ronald Ping Davion Jimenez Mohammed Hausman Marleigh Zukowski Jeffrey Linkous Ellen Lucy Judah Anderson Ellen Pettiford Meredith Ferri Chelsea King Mckenna Panek Reign Esch Madilyn Mcelrath Arjun Buhler Eloise

Sign in to post a comment.


Sign In