




Hon. Salisu Muktari Ya Bada Tallafin Karatu Ga Marayu Hudu A Makarantar Flying Colors International Academy Potiskum
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
1 day ago
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya bayar da tallafin karatu kyauta ga marayu guda hudu da marasa galihu a makarantar Flying Colors International Academy da ke karamar hukumar Potiskum.
Shugaban zartarwar ya dauki nauyin karatun dalibai hudun ne, yayin da mai magana da yawunsa (Mataki na musamman na Sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum), Ibrahim M. Nura, ya yi jawabi a madadinsa yayin bikin yaye dalibai a harabar makarantar a yau Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025.
“Kamar yadda nake magana a madadin shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, duk da cewa ina nan ne a matsayin uba kuma Dan'uwa ga ’yan uwana mata guda biyu, zan yi amfani da wannan damar wajen koyi da maigidana kuma shugabana, Hon. Salisu Muktari, wajen daukar nauyin kudin makaranta na marayu hudu da marasa galihu.
“Ina ba da umarni ga wannan hukumar gudanarwar makarantar da su zakulo yara marayu hudu da marasa galihu domin mu biya musu kudin makaranta a madadin shugaban zartarwa na karamar hukumarmu mai albarka Hon. Salisu Muktari, wannan din koyi ne na irin ayyukan alheri da shugaban karamar hukumar yake yi a kodayaushe, musamman a fannin daukar nauyin karatun marayu da marasa galihu" Inji Ibrahim M. Nura.
Shugaban ya kasance yana daukar nauyin karatun marayu a matakai daban-daban, kuma a baya-bayan nan ya dauki nauyin karatun wani maraya don karantar MBBS a Jami’ar Maiduguri.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.



