

Hon. Salisu Muktari, jagorancin sa ya habaka noma, Lafiya, da farfado da karamar hukumar Potiskum.
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
13 days ago
... Yunkurin da ke nuna kwazonsa na tabbatar da Alkawarin Gwamna Buni FCIA, CON, COMN.
.
.
Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya zama jajirtacce gurin bunkasa noma, lafiya, da kuma farfado da karamar hukumar Potiskum.
Hakan dai ya yi daidai da jajircewarsa na ganin ya tabbatar da kudirin gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna H.E. Mai Mala Buni na bunkasa sassan da samar da ingantaccen tattalin arziki tare da inganci da jaha zata samu dogaro da kai a nan gaba.
Hon. Salisu Muktari ya cancanci lambar yabo ta _ Gwarzon Noma, Lafiya da Gine-gine da samar da sabuwar karamar hukumar Potiskum biyo bayan jajircewarsa na ganin al'amura sun tafi daidai a kowane bangare.
Hon. Salisu Muktari yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da alkaluman da suka nuna cewa karamar hukumar Potiskum ta zarce takwarorinta na jihar Yobe a fannin kiwon lafiya saboda irin gudumawa da goyon bayan da yake baiwa fannin a kowane lokaci da kuma yadda yake sa ido tare da tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin inganci.
Hakazalika, a fannin noma, ya himmatu wajen bayar da cikakken gudunmawar sa wajen inganta ayyukansu da kuma kawo ci gaba da zai nuna jihar Yobe a matsayin jiha mai tasiri sosai a fannin noma da kuma karamar hukumar Potiskum a matsayin zakaran karamar hukuma a fadin jihar Yobe.
Shugaban karamar hukumar Potiskum ya himmatu wajen kawo sauyi a karamar hukumar Potiskum ta hanyar farfado da dukiyar/kadarorin gwamnati da aka yi watsi da su tare da tabbatar da ingancinsu da sabunta su a fadin karamar hukumar Potiskum.
“Potiskum ta fi ko’ina a gare ni, kuma za mu tsaya tsayin daka don ganin mun samar da ci gaban da zai sa mu da duk masu son ci gaban karamar hukumar yin alfahari.” inji shi
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

