Hanyoyi: Hon. Salisu Muktari zai gina sabbin hanyoyi uku da sabbin gadoji biyu a karamar hukumar Potiskum
ibrahim muhammad nura
Image

Hanyoyi: Hon. Salisu Muktari zai gina sabbin hanyoyi uku da sabbin gadoji biyu a karamar hukumar Potiskum

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

1 month ago

Shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari ya samar da sabbin ayyukan tituna guda 3 da sabbin gadoji 2 daga hukumar farfado da arewa maso gabashin Najeriya (NEDC).

Shugaban karamar hukumar ya je hukumar NEDC Abuja musamman domin farauto sabbin hanyoyi guda 3 da sabbin gadoji 2 izuwa karamar hukumar Potiskum domin ingantawa da kuma samar da saukin zirga zirga ga al'ummar yankunan da ke karamar hukumar potiskum.

A yayin da shugaban karamar hukumar ke bayyana nasarar da ya samu na samar da hanyoyin guda uku da gadoji biyu, ya tabbatar da cewa:

“Karamar hukumar Potiskum gida ce kuma ginshiki a gare mu baki daya, haka nan dole ne mu yi alfahari da al’ummarmu kuma ya zama wajibi mu tashi tsaye wajen samar da manufofin da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikinmu, samar da Hanyoyi ga al'ummominmu za su taimaka sosai wajen bunkasa tattalin arzikinmu da samar da hanyoyi masu sauki don gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.

“Hukumar ci gaban Arewa maso Gabashin Najeriya NEDC, za ta taimaka wajen gina da samar da hanyoyi uku da gadoji biyu wadanda za su hade wasu yankunan da kuma saukaka tafiye-tafiye ga al’ummar yankunan.” Hon. Salisu Muktari ya tabbatar

Sabbin hanyoyin sun hada da Kwanan Danja zuwa Nasarawa da ke hanyar Maiduguri, Tashan Gawo zuwa Anguwar Jaji, Misau road zuwa Lailai duk a karamar hukumar Potiskum.

Haka kuma manyan gadoji guda biyu za su hada Tashar Gawo da Anguwar Jaji sai kuma Wanda zai hada Misau road da anguwar Lailai, wadannan wuraren da magudanar ruwa ta katse su na tsawon lokaci za su samu saukin tafiye tafiye bayan kafa wadannan manyan gadoji guda biyu.

Shugaban karamar hukumar ya tabbatar da cewa hukumar ta tabbatar da yin aiki mai inganci tare da kammala shi a lokacin da ya dace.

Mal. Ibrahim Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

176
2633
1 month ago

ibrahim muhammad nura

Sign in to post a comment.


Sign In