




Gyara Da Sauya Fasalin Garin Damaturu: Shirye Shirye Na Karfafa Jihar Yobe Da Inganta Ci gaban Tattalin Arzikinta
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
6 days ago
Gwamna Buni ya himmantu wajen aiwatar da aikin sake Sauya Fasali da raya birnin Damaturu, shirin da zai karfafa jihar Yobe da inganta tattalin arzikinta.
Jihar Yobe tsohuwar jiha ce da ke da tasiri a bangarori da dama da ke bukatar kawo taswirarta a babban birnin jihar domin bunkasa albarkatun jihar da wayar da kan masu yawon bude ido, wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen jawo masu zuba hanun jari.
Aikin bunkasa Babban birnin jihar da Gwamnan Jihar Yobe H.E. Hon. (Dr.) Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ya himmantu wajen gudanar da ayyukan da suka hada da gina babbar gadar sama da gadar karkashin kasa ta farko a jihar Yobe___ "Flyover and Underpass Bridge" da kuma gyaran tsoffin zagayen shatale-talen da aka yi amfani da su don ado da kyau kawai a da.
Gwamna Buni ya zabi yin amfani da sauye-sauyen da ake gudanar wa a Damaturu domin baje kolin tarihi, al'adu, da tattalin arzikin jihar Yobe cikin taswirar zane, wanda hakan zai yi tasiri wajen jawo hankulan maziyartan jihar su zuba jari a cikin albarkatun jihar Yobe.
Babban birnin kowace jiha alama ce ta nuni ga arziki da ci gaban jihar, kuma matakin da Gwamna Buni ya dauka na bayyana fasalin tattalin arziki cikin taswirar gine-ginen shatale-talen cikin garin Damaturu zai ba da dama ga masu zuba jari su san da albarkatun jihar da kuma basu sha'awar ziyartar albarkatun kasa na jihar don kulla yarjejeniyar Kasuwanci.
Jihar Yobe tana da damar jawo hankalin masu yawon bude ido zuwa wuraren yawon bude ido da wuraren shakatawa daban-daban, wadanda za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki; don haka shawarar zayyana taswirar jirgin ruwan Dufuna a daya daga cikin shatale-tale a Damaturu zai yi tasiri gurin nuna tarihi don zuwa yawon bude ido.
Nuna irin waɗannan albarkatu zai ƙarfafa baƙi su buɗe idanunsu da jawo masu zuba jari don samun damar albarkatun ƙasa da haɓaka kasuwancin ƙasa da ƙasa.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.














3 days ago