Gwamnatin mu ta dukufa gurin Samar da ababen more rayuwa don inganta tattalin arziki _Gov. Buni ya shaida wa wakiliyar UNDP
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
1 month ago
Gwamnan jihar Yobe H.E Hon. Mai Mala Buni CON COMN ya shaida wa wakiliyar kungiyar Raya kasashe na majalisar dinkin duniya (UNDP) Ms Elsie Attafuah cewa gwamnatin sa na aiki tukuru don farfado da tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya shaida Mata hakanne a yayin wani ziyarar ban girma da wakiliyar ta Kai masa, inda yace Gwamnatin sa zata binciko dumbin albarkatun noma da kiwo da sauran albarkatun kasa da ke fadin jihar domin samun damammakin zuba jari don bunkasa kasuwanci a fadin jihar.
Ya cigaba da bayyana cewa a kwanakin baya gwamnatin jihar ta mayar da hankali kan shirye shiryen gyare gyare da kuma farfado da kadarorin gwamnati da al'ummomin da rikicin Boko-Haram ya shafa.
"Bisa ingancin harkokin tsaro a jihar mu a yanzu, muna duba da Kiran masu zuba hanun jari tare da yin amfani da abubuwan da ake dasu a jihar don bunkasa hanyoyin zuba jarin." Cewar Gwamnan.
Ya kuma tabbatar da cewa Jihar Yobe tana Kan gaba gurin moman Rid'i da kiwo a fadin najeriya, sannan ya tabbatar da gwamnatin sa zata zuba hannun jari a bangarorin guda biyu don ganin jihar Yobe ta zama cibiyar fitar da Rid'i da dabbobin kiwo a kasashen duniya.
"A matsayin jihar Yobe jiha ta biyu da sukayi fama da matsanancin hare-haren ta'addancin Boko-Haram, jihar bata samun wadatacccen tallafi daga abokan huld'a saboda kalubalen da yake tattare da samun damar shigowa Jihar.
"Yanzu muna da filin jirgi mai aiki, abokan cinikayya yanzu za su iya shiga cikin jihar mu cikin sauki kuma suyi kasuwanci da kyakkyawan mu'amalar kasuwanci da jama'ar sannan nasan zasuji dadin kasancewar su a jihar saboda dawowan tsaro Mai inganci jihar." Inji Gwamna Buni
A bangaren wakiliyar kungiyar Raya kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP Ms Elsie Attafuah ta tabbatar da cewa ta yaba da kokarin Gwamnatin Hon. Mai Mala Buni CON na farfado da tattalin arziki da samar da sake tsugunar da al'ummar jihar a mazaunan su.
Sannan tayi nuni da cewa UNDP na son hada gwiwa da Gwamna jihar a fannonin ci gaba da suka hada da zuba jari da kuma bayar da tallafi na musamman ga al'ummar da matsalar tsaron ya shafa.
Mal. Ibrahim M Nura
Special Assistant on Information and communication to the executive chairman of Potiskum local government area.