Gwamna Buni ya kai ziyarar bazata zuwa Kasuwar Zamani na Ngalda... Ya nuna gamsuwa da aikin
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Gwamna Buni ya kai ziyarar bazata zuwa Kasuwar Zamani na Ngalda... Ya nuna gamsuwa da aikin

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

14 days ago

Gwamnan jihar Yobe, H.E. Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, ya kai ziyarar bazata zuwa aikin kasuwan zamani na Ngalda, inda ya nuna gamsuwar sa da aikin, kuma ya bada tabbacin kammala aikin a kan kari akan lokaci.

Gwamnan wanda ke tare da mataimakinsa, Hon. Idi Barde Gubana, ya bayyana gamsuwarsa da kuma kwarin gwiwa kan ingancin aikin kasuwan.

“Na gamsu sosai da ka’idojin wannan aikin, kuma dole ne dan kwangilar ya nuna jajircewa wajen ganin an kammala kasuwar cikin wa’adin kwangilar da aka kayyade.

“Kasancewar kasuwar Ngalda na da matukar tasiri da inganci ga wadanda ke gudanar da ayyukansu a karkashin tsarin wucin gadi, gwamnatinmu ta gina wannan kasuwa ne domin samar da yanayi mai aminci da wadata ga harkokin kasuwanci da karfafawa da fadada tattalin arzikin jihar.

“Gwamnatinmu tana gina irin wadannan kasuwanni a garuruwan Yunusari da Machina domin tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arziki a yankunan da jihar baki daya.

“Ina kira ga jama’a da su tabbatar da ingancin kasuwar tare da tabbatar da kula da yadda ya kamata domin jama’a da gwamnatin jiha su amfana ta fuskar tattalin arziki daga karuwar hanyoyin samun kudin shiga na zamani." Inji Shi

Kwamishinan gidaje na jihar Yobe, Arch. Ahmed Buba Kyari, wanda ke wajen a yayin ziyarar, ya ce dan kwangilar ya gudanar da aikin ne bisa ka’ida da kayyade lokacin kwangilar.

Ya kuma tabbatar da cewa aikin yana kan matakin karshe kuma za a kaddamar da shi nan da kankanin lokaci.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

15
234
14 days ago

Sign in to post a comment.


Sign In