Gwamna Buni Ya Amince Da Karin Naira Dubu Goma A Duk Wata Ga ‘Yan Fansho Na Kananan Hukumomi
ibrahim muhammad nura
Image

Gwamna Buni Ya Amince Da Karin Naira Dubu Goma A Duk Wata Ga ‘Yan Fansho Na Kananan Hukumomi

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

11 days ago

... Yunkurin da zai daidaita kudaden da suke samu tare da samar musu wadataccen kashe kudi.


Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, FCIA, CON, COMN, ya amince da karin biyan Naira dubu goma duk wata ga daukacin ‘yan fansho na kananan hukumomin jihar Yobe.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jihar Yobe ta fitar, inda ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin mai girma Gwamna Hon. Mai Mala Buni ya amince da karin biyan Naira dubu goma ga daukacin ‘yan fansho na kananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya himmatu wajen tabbatar da ingancin rayuwa da walwalar ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa a jihar da ma wadanda suka yi ritaya suka zama ‘yan fansho.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya amince da karin mafi karancin albashin ma’aikatan kananan hukumomin domin inganta hanyoyin samun kudaden shiga da kuma tabbatar da jin dadin su.

“Rayuwar wadanda suka yi wa al’ummarmu aiki da karfinsu da lokacinsu, wato ‘yan fansho, abin ya dame mu, zai yi kyau idan muka kara musu albashi domin su rayu cikin kwanciyar hankali.” Yace

Gwamnan ya jajirce wajen ganin an samu zaman lafiya da walwalar ma'aikatan jihar Yobe.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

18
277
11 days ago

Cheshire Ander

Sign in to post a comment.


Sign In