

Gwamna Buni ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 267 aiki na dindindin
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
23 days ago
... 140 daga cikinsu sun kammala karatun digiri na farko a karkashin Gov. Buni Scholarship a Indiya.
•
•
Gwamnan jihar Yobe, H.E. Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 267 na dindindin domin inganta fannin kiwon lafiya da samar da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Hakan ya yi daidai da kudurin gwamnan na samar da ayyukan yi, bunkasa harkokin kiwon lafiya, da samarwa al’ummar jihar Yobe kwararru da ingantattun likitocin zamani.
Daga cikin ma’aikatan lafiya 267 da za a dauka, 140 daga daliban da gwamna ya dauki nauyin karatunsu a kasar Indiya (Buni Schoolers), wadanda suka yi karatu a fannonin kiwon lafiya daban-daban kuma suka samu kwarewa da gogewa ta musamman da na zamani.
Daga cikin daliban da Gwamna ya biya kudin karatu zuwa kasashen waje (Buni's Schoolers) da suka samu damar zama ma’aikata na dindindin, sun samu kwarewa a fannoni kamar haka: 43 BSc Nursing, 43 BSc Pharmacy, 22 BSc Laboratory Science, BSc Radiology 24, BSc Optometry 7, da kuma BSc Public Health guda 1.
Haka kuma, karin masu aikin sa kai 127 sun fito ne daga cibiyoyin lafiya daban-daban na jihar, kamar yadda gwamnan ya ce ya kamata a dauki ma’aikata 127 masu aikin sa kai (volunteers) a matsayin ma’aikata na dindindin.
Gwamnan ya ba da umarnin daukar masu aikin sa kai ne saboda kwarewa da gogewar da suke da su wajen mu’amala da marasa lafiya da sanin aiki bayan sun kammala karatunsu a baya.
Wadanda aka zaba a karkashin (Buni's Schoolers) an sanya su a matakin CONHESS 8; Hakanan, an sanya masu aikin sa kai a CONHESS 6/2 kamar yadda gwamna ya umarta.
Gwamna Buni ya himmatu wajen inganta harkar lafiya da ilimi ta hanyar daukar sabbin ma’aikata a sassan guda biyu.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na musamman akan yada labarai da sadarwa ga shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum.

10 days ago

1 day ago

1 day ago