Gwamna Buni tare da rakiyar amininsa, Hon. Salisu Muktari, ya kai ziyarar bazata ga ayyukan da ake gudanarwa a Damaturu
ibrahim muhammad nura
Image
Image
Image
Image

Gwamna Buni tare da rakiyar amininsa, Hon. Salisu Muktari, ya kai ziyarar bazata ga ayyukan da ake gudanarwa a Damaturu

ibrahim muhammad nura
@muhammadnuraibrahim848393

10 days ago

... Wannan ziyara ne don tabbatar da ingancin ayyukan da kuma tabbatar da cewa aikin yayi daidai da yarjejeniyar kwangilar da aka bayar.
.
.
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, tare da rakiyar babban amininsa, shugaban zartarwa na karamar hukumar Potiskum, Hon. Salisu Muktari, ya kai ziyarar bazata ga aikin titin Maisandari zuwa Gambir da kuma aikin titin Maduri-Benkalio da Don Etibet a Damaturu.

Gwamnan ya kai ziyarar bazata tare da babban amininsa Hon. Salisu Muktari, don tabbatar da ingancin aikin da kuma tabbatar da aikin ya yi daidai da yarjejeniyar kwangilar.

A yayin ziyarar gwamnan ya yi kira da a tabbatar da an kammala aikin cikin lokacin da aka kayyade tare da zaburarwa da yin kira ga ‘yan kwangilar da su tabbatar sun yi aiki mai inganci.

“Dole ne a tabbatar da ingancin wannan aiki, kuma a kammala shi a kan lokaci daidai da yarjejeniyar kwangilar da muka kulla, domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci zai kara mana kwarin guiwa da tabbatar da alkawurran da mukayi ga al’ummar jihar Yobe.” Yace

Gwamnan ya kuma yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta jihar da ta tabbatar da ci gaba da sanya ido kan ayyukan domin tabbatar da ingancinsu da kuma tabbatar da kammala ayyukan a kan lokaci.

“Na umarci ma’aikatar ayyukanmu ta Jihar Yobe da ta ci gaba da sanya ido kan ayyukan da ake gudanarwa a fadin jihar Yobe domin tabbatar da ingancinsu da kuma tabbatar da kammala dukkan ayyukan mu a kan lokaci.

“Na kuma umurci ma’aikatar ayyuka ta jihar Yobe da ta ci gaba da sanya ido a kan wadannan ayyuka domin tabbatar da ingancinsu da kuma tabbatar da an kammala ayyukan bisa yarjejeniyar da muka yi a lokacin da muke ba da kwangilolin, domin dole ne mu tabbatar da ingancin ayyukan da muka gabatar domin ci gaban mutanenmu nagari.” Gwamna Buni ya kara da cewa

Ziyarar tare da amininsa Hon. Salisu Muktari alama ce ta amanar da ke tsakaninsu bisa gaskiya da rikon amana.

Hon. Salisu Muktari da Gwamna Mai Mala Buni tsuntsaye ne guda biyu masu fuka-fuki daya.

Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.

131
1971
10 days ago

Murguia Monroe Gilmartin Zahir Ramirez Amias Walker Eliel Gonzales Ramon Hernandez Kaiser Nelson Jadiel Roberts Ronan Garzon Mabel Ping Louise

Sign in to post a comment.


Sign In