

Bankin Duniya ya yabawa Gwamna Buni, ya baiwa Gwamnatin Jihar Yobe kyautar Naira Biliyan 5 kan bin ka'idojin kashe kudi
ibrahim muhammad nura@muhammadnuraibrahim848393
3 days ago
… Gwamna Buni ya himmatu wajen tabbatar da jin dadin mazauna jihar ta hanyar saka hannun jari a fannin kiwon lafiya, noma, kiwo, da ilimi.
.
.
Bankin Duniya ya yabawa Gwamna Buni tare da baiwa Gwamnatin Jihar Yobe kyautar Naira Biliyan 5 kan ladabtar da hanyoyin kashe kasafin kudi.
Bankin Duniya, a karkashin “State Fiscal Transparency Accountability and Sustainability Program From Results (SFTAS)” ya sanya jihar Yobe a matsayin jiha ta farko da take kashe kudaden al’umma ta hanyar da ta dace ba tare da wata matsala ba, shi ya sa ta amince da jihar, kuma jihar ta samu kyautar Naira biliyan 5 na bana.
Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin mai girma gwamna Hon. Mai Mala Buni FCIA, CON, COMN, ta himmatu wajen tabbatar da jin dadin al’ummar jihar ta hanyar saka hannun jari a fannin kiwon lafiya, noma, kiwo, ilimi, da sauran bangarorin ci gaban jihar, gami da ayyukan more rayuwa na zamani wadanda zasu dace da fasahar zamani.
Jihar Yobe ta samu kwanciyar hankali na tattalin arziki da zamantakewa da siyasa da ba a taba ganin irinsa ba a karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna Hon. Mai Mala Buni FCIA CON COMN.
Wata sanarwa da bankin duniya ya fitar ta bayyana cewa;
“A binciken da hukumar SFTAS ta gudanar, bankin mu ya tabbatar da cewa jihar Yobe ita ce ta farko wajen adana kadarorin al’umma da kuma kashe su ta hanyar da ta dace wajen saka hannun jari a rayuwar al’umma domin inganta makomarsu a cikin jihohi 36 na Nijeriya.
"Wannan kuma shine dalilin da ya sa jihar ta samu kyautar Naira biliyan 5 da aka bayar a bana." Sanarwar bankin ta ce
Gwamna Buni, FCIA, CON, COMN, ya himmatu wajen inganta rayuwar al’umma, musamman matasa, domin tabbatar da jin dadin mazauna jihar ta hanyar da ta dace.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki na Musamman akan Watsa Labarai da Sadarwa ga Shugaban Zartarwa na Karamar Hukumar Potiskum.


