
Media Aide — Muryar da Ke Gina Mutunci ko Lalata Hoton Dan Siyasa Koh Mai Mulki a Kafafen Sada Zumunta
Potiskum LGA Eyes@muhammadnuraibrahim848393
1 month ago
Lokaci Ya Yi Da Masu Aikin Sadarwar Siyasa Zasu Zama Masu Gina Labari, Ba Masu Shiga Hayaniya Ba
A zamanin da kafafen sada zumunta suka zama tushen labari da ra’ayoyi, aikin Media Aide ya wuce rubutu da daukar hoto kawai, a yanzu shi ne ginshiƙin da ke gina ko rushe hoton ɗan siyasa a idon jama’a.
A yau, jama’a ba sa jiran jaridu ko rediyo kafin su yanke hukunci, abin da suka gani a Facebook, suka karanta a X (Twitter), ko suka kalla a TikTok, shi ke gina tunaninsu game da shugabanni. Wannan ne ya sa aikin Media Aide ya zama na dabaru, hikima, da ingantaccen tsari ba na hayaniya ko mayar da martani cikin fushi ba.
Media Aide mai nagarta yana gina labari cikin natsuwa, yana bayyana nasarorin gwamnati da hangen nesan shugabansa cikin harshen da jama’a ke fahimta da yarda da shi, shi ne mai kare martaba ba tare da bata suna ba, mai tsara sakonni da salo, kuma mai tafiyar da magana cikin ladabi da hankali.
Amma wanda bai san nauyin wannan mukami ba, yana iya jawo wa gwamnati sukar da ba ta da tushe, ko ma lalata sunan ɗan siyasar da yake wakilta, wannan ba kawai rashin kwarewa ba ne, illa ce ga tasirin gwamnati a idon al’umma.
Don haka, masu rike da mukamin SSA on Media da sauran jami’an yada labarai a matakin gwamnati, ya kamata su gane cewa aikin su ba fafutukar gardama ba ne, bayyana ayyukan gwamnati su ne hujjar su, kuma ana bukatar su bayyana su da hikima, da tsari, ba da hayaniya ba.
A duniyar siyasa ta yau, wanda ya mallaki dabarun sadarwa shi ne ke mallakar zukatan jama’a, saboda haka, Media Aide mai nasara shi ne wanda yake gina labari, ba wanda yake shiga hayaniya ba.
Mal. Ibrahim M. Nura
Mataimaki Na Musamman Kan Yada Labaru Da Sadarwa
Ofishin Shugaban Karamar Hukumar Potiskum.
1 month ago
1 month ago
1 month ago
1 month ago
25 days ago
25 days ago
24 days ago
16 days ago
16 days ago
13 days ago
9 days ago